Kada Wanda Yakara Cewa Bazawara Manzon Allah (S) ya Auri Nana Khadeejart (As)..!!


Nana Khadeejart budurwa ce ba Bazawara ba..!!
_______________________
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
"Fas'aluu ahlaz-zikri in kuntum laa
ta'lamun" (Suratun-nahl: 43)
sadaqallahul-aliyyul-azeem.

Hakika idan muka dauki tarihi
muka shimfida shi a gaban mu
zamu taras bai bamu tsantsar
rayuwar Nana Khadijah filla-filla
ba kafin auren ta da Annabi
Muhammad (sallallahu alaihi wa
alihi). Sai dai yayin da muka
karkata zuwa hannun mu na hagu
zamu iske akwai ruwayoyin da
suke nuni akan cewar tayi aure
kafin ta auri Manzon tsira (S) da
mazaje biyu, wanda shine ake
ruwaitowar ta haifi wasu 'Yayayen
da su wato Atiqu bn Aa'id Al-
makhzuumiy da Abu-haalata At-
tamiimiy. Wanda idan kana son
kaga bambamce-bambamce akan
irin wadannan ruwayoyin ka duba:
Al-isaabah: 3/611, As-siiratul-
halabiyyah: 1/140, Usudul-ghaabah:
5/71 da 121.

Haka nan dai yayin da muka waiga
barin mu na dama zamu taras
akwai "Masaadir" daban da suke
ruwaitowa hakika Annabi
Muhammad (S) lokacin da ya auri
Nana Khadijah ta kasance budurwa
ne ba wai bazawara ba. Wanda a
wadannan ruwayoyin sai suke
tabbatar da cewar Zainab da
Ruqayya 'Yaya ne na Haalah
'Yar'uwar Khadijah wadanda
Khadijan tayi tabannin su bayan
da suka rasa mahaifiyar su. Ka
duba cikin "Manaaqib Aali Abi
Talib: 1/159, haka nan dai ka duba
littafin A'lamul-hidaayah juzu'in sa
na 3, da As-sahihu min siiratun-
Nabiyyul-a'zam (S): 1/121 – 126.

Nana Khadijah (alaihas-salam),
abinda tarihi yake tabbatar wa
akan ta shine; ta kasance daga
cikin mafifitan matan quraishawa
daraja, da mafifitan su dukiya, da
kyau. Ta kasance ana kiranta tun a
jahiliyya da "Taahirah", haka nan
dai ana ce mata "Sayyidatu
quraysh". Kuma dukkanin mutanen
ta sun nemi auren ta wanda suka
saki dukiya mai yawa amma taki
yarda da ta auri kowa. Ka duba
cikin: Al-bidayah wan-nihayah
juz'in sa na 2 shafi na 294, da
Bahjatul-mahaafil juzu'in sa na 1
shafi na 48, da Siratun- Nabawiyyah na Ibn Hisham juzu'in
sa na 1 shafi na 201, da Tarikhul-
khamis juzu'insa na 1 shafi na 263,
da Tabaqat na Ibn Sa'ad juzu'insa
na 1 shafi na 131, da Siratul-
halabiyyah juzu'insa na 1 shafi na
137, da Siratun-Nabawiyyah na
Dahlan juzu'insa na 1 shafi na 55.

Hakika manyan quraishawa sun
nemi auren Nana Khadijah
(alaihas-salam) wadanda suka yi
iya kokarin su da shimfida mata
dukiya, wanda daga cikin su akwai
Uqbah bn Abi Mu'it, da Sult bn Abi
Yahaab, da Abu jahal, da Abu
Sufyan wanda duk taki su gaba
daya, ta zabi fiyayyen halitta
(sallallahu alaihi wa Alihi). Haka
nan Magana akan wai Amminta
Amru bn Asad yayi mata baiko
"Huduba" da Warqata bn Naufal,
da ammin ta a tare, ko kuma
Waraqatan shi kadai bai inganta
ba sam-sam. Duba cikin Al-bihaar
juzu'insa na 16 shafi na 19 daga
Waaqidiy, da Siratul-halabiyya
juzu'insa na1 shafi na 129 da shafi
na 137.

Abinda ainahin tarihi ma ya
tabbatar shine kwata-kwata babu
ma wani mutum wai shi Waraqata
bn Naufal balle ma ya zamo wani
Ammi ga Nana Khadija (alaihas-
salam).

Malam Baihaqiy ya inganta
wannan Magana akan Manzo (S)
ya auri Nana Khadijah tana da
shekaru 25 a duniya a cikin
littafinsa na Dala'ilun-nubuwwah
juzu'insa na 2 shafi na 71, da
Bidaayah wan-nihayah juzu'insa
na 2 shafi na 294 da 295, da
Muhammadun Rasulullah,
Siiratuhu wa atharuhu fil-hadarah
shafi na 45, da Siiratun-
nabawiyyah na Ibn Kathir
juzu'insa na 1 shafi na 265, da
Siiratul-halabiyyah juzu'insa na 1
shafi na 140. wasu sun ruwaito
akan tana da shekaru 28, wasu
kuwa shekaru 30, wasu shekaru 35,
wasu shekaru 40, wasu shekaru 44,
wasu shekaru 45, wasu 46.

Yayin da muke cewa anyiwa
Musulunci baki dayan sa cuse na
abinda aka so daga makiya
addinin da Annabi Muhammad (S),
wasu kan yi mamakin haka har su
fadi munanan maganganu ba tare
da bincikawa wajen taras da
gaskiyar abinda muka fada ba!
Yaya zakace da maganar da tazo
cikin Siiratuul-halabiyya juzu'insa
na 1 shafi na 140, akan cewa wai
Manzon Allah (S) ya shiga wajen
Khadijah kafin ya aure ta, ta kama
hannun sa ta rungume a kirjin ta
([colo=red]wal-iyazu billa) da ire-
iren su na ban mamaki da
bakunta?! Haka nan ya zaka ce a
irin maganganun da ake cewa
Manzo (S) wai ya aure ta ne don
kwadayin kudinta "innamaa
tazawwaja Khadijah tama'an fiy
maliha" wanda wannan kalma
"Tama'an" tana nufin Kwadayi
musamman na kudi "Cupidity,
greed". Ka duba cikin littafin An-
nubuwwah talifin Sheikh
Muhammad Hasan Aali Yaasin
shafi na 63.

Yana daga cikin abinda Ahlus-
sunna suke ruwaitowa na zubarwa
da Annabinmu Muhammad
mutunci a cikin bada tarihin sa.
Akwai irin abubuwan da ake
ruwaitowa wai lokacin da Manzon
Allah (S) suka yi tafiya Safara da
yaron Nana Khadija (A) bayan
abubuwan da suka bayyana na
Mu'ujiza daga Annabi (S) shi yaron
nata wato Maisara da suka dawo
duk ya gaya mata. Wanda taje
wajen 'dan amminta Waraqata bn
Naufal take bashi labari yake cewa
idan har hakan ta tabbata to lallai
shine Annabin wannan al'umma.
Haka nan da irin yadda Manzo
farkon fara yi masa wahayi a dai
ruwayar Ahlus-sunnan bayan ya
dawo gida yana cewa da Nana
Khadija (A) "dath-thiriiniy" ……..
daga karshe shima wai taje wajen
Warqata bn Naufal din take gaya
masa ga abinda ya faru shima nan
yake cewa ai lallai Annabi ne.
Haka nan dai a lokacin da yazo
gida Annabin tsiran (S) ya bata
labari ga abinda ya faru shine ta
cire dankwalin ta ta tambayi
Manzo (S) shin yana cigaba da
ganin mutumin yace baya ganin
sa, don haka ta nan ne ta gano
cewar lallai Mala'ika ne ba
Shaidan ne ba. Wato shi kansa
Manzon (S) bai ma san da wa yayi
Magana ba a can kogon!!! Wannan
wadanne irin "Khuraafat" ne
ayyuhal-musliminal-a'izza'?!
"haihaata haihaata an yattasifa
Nabiyyunal-akram bi hazihis-sifa
wa bihaazash-shakl".

Shin da gaske ne Khadijah (A)
bazawara ce Annabi (S) ya aura?
Hakika muna da shakku mu
mabiya Ahlul-bait (A) akan cewar
tayi aure kafin Manzon tsira ya
aure ta. Wanda kamar yadda baya
kadan na kawo ana ruwaitowa da
ta auri mazaje biyu har ta haifi
'Yayaye da su wato sune Atiqu bn
A'iz bn Abdullahil-makhzumiy da
Abu Haalatat-tamiimiy. Wanda
muke matukar shakku akan
wannan maganar wacce bata da
wani tushe illa Siyasa ce ta dasa
wannan Magana. Ban son na dan
ja Magana akan sassabawar su
akan ma Abi Halata din. Shin shine
An-nabaash dan Zaraarata ko
kuwa ba shi ba ne, ko kuwa shine
Hindu, ko Maalik, shin ma shi
Sahabi ne ko a'a, kuma shin ta
aure shi ne kafin Atiq, ko kuwa
Atiqun ta aura kafin sa?! Ka duba
cikin littafin Awaa'il juzu'insa na 1
a hamishin shafi na 159.
Haka nan da yin Magana akan
shin samuwar shi Hindun da
Khadijah ta Haifa dan wannan
auren ne ko wancen, idan har ya
kasance dan Atiqu ne to zai zamo
mace ne (kamar yadda yazo a
cikin Awaa'il juzu'insa na 1 shafi
159, inda yake cewa wannan
Hindun ce dai Saifiy bn Aa'iz ya
aura suka haifi Muhammad bn
Saifiy) to idan kuwa ba haka bane
to namiji ne. Shin an kashe shine
tare da Aliy a yakin Jamal, ko
kuwa ya mutu a sanadin fari a
Basra?! Idan kana son ganin irin
wadannan sassabawar da wasun
su ka duba: Al-isabah juz'insa na 3
shafi na 611/612, da Nasabu
Quraish na Mus'abuz-zubairiy shafi
na 22, da Siiratul-halabiyyah
juzu'insa na 1 shafi na 140, da
Qaamusur-rijaal juzu'insa na 10
shafi na 431, da Naql anil-balaziriy
da Usudul-ghabah juzu'i na 5 shafi
na 12/13 da 71, da wasun
wadannan "Masaadir".
Ban son tsawaitawa akan haka
amma zan kawo wadannan
mulahazozin:
•Ibn Shahr Aashuubiy ya fada:
"Ahmad Balaziriy ya ruwaito, da
Abul-qasim Al-kuufiy a cikin
litattafan su, da Murtadha cikin
Ash-shaafiy, da Abu Ja'afar cikin
At-talkhis cewa: hakika Annabi
(sallallahu alaihi wa Alihi) ya aure
ta (Khadijah), alhalin ta kasance
"AL-AZRA'U" wato budurwa,
wanda ko a yaren turanci ma'anar
Azra'u shne "Virgin, maid, vestal"
wanda dai dukkanin su suna bada
ma'ana ne akan macen da bata
taba aure ba. Wanda abinda aka
ambata cikin littafin Al-anwar da
Al-bida'u yana karfafa hakan
cewar: Ruqayya da Zainab sun
kasance 'Yayaye ne ga Haalah
'Yar'uwar Khadijah". (wanda
wadannan litattafan ma sun fitar:
Manaaqib Aali Abiy Talib juzu'insa
na 1 shafi na 159, da Al-bihhar: da
Rijalul-maamaqaaniy, da
Qaamuusur-rijal).

•Abul-qaasim Al-kuufiy ya fada
cewar: "hakika abinda yake ijma'i
daga abinda yake daga kebantattu
da gaba daya, daga ma'abota tarihi
da naqalto labarai, akan cewar bai
rage daga cikin masu girma da
darajar Quraishawa ba, da
shugabanninsu da ma'abota
wadata daga cikinsu, sai da ya
nemi auren Khadijah, kuma yaso
auren ta, amma taki amincewa da
hakan daga gaba dayan su ba.
Yayin da Manzon Allah (S) ya aure
ta matayen Quyraishawa sun ji
haushin ta kuma sun kaurace
mata, suka ce mata: manya-
manyan Quraishawa da Sarakunan
su sun nemi auren ki baki auri
daya daga cikin su ba. Sannan ki
auri Muhammad marayan Abu
Talib, faqiri, wanda bashi da
dukiya?!
Da wadannan takaitattun kalmomi
nake son mu fahimci cewar lallai
abinda yake tabbatacce tsakanin
Shi'a da Sunna shine kasantuwar
Nana Khadijah (alaihas-salam)
budurwa babu wani 'da da ya taba
auren ta, Manzon Allah Annabi
Muhammad (S) shine mijinta na
fari kuma shine na karshe. Hakika
addinin musulunci abu ne mai
fadin gaske, kuma an yiwa tarihin
musulunci illa matuka da gaske
daga dashen makiya addinin da
Manzon. Kamar yadda yake
tabbatacce ga dukkanin firkokin
musulunci bayan wafatin Manzon
tsira an bi ana ta kone hadisan
Annabi (S) da hujjar "kafaanaa
kitaabullah", inda gaba daya aka
hana ruwayar hadisai. Kuma ba'a
fara yin tadwiiinin hadisai ba sai a
lokacin Halifan Umawiyyawa Umar
bn Abdul-aziz. Don haka wannan
addinin cike yake da ninkiya da
dungu.

Babu mamaki ga wanda karatun sa
ko binciken sa bai kai kan wannan
mas'ala da sabani akan
kasancewar Nana Khadijah
budurwa ce lokacin da Manzon
Allah (sallallahu alaihi wa Alihi) ya
aure ta, tare kuma da karancin
shekarun ta wadanda basu kai
sanannen adadin da ammawa suka
fi sani ba na shekaru (45). Babban
abinda yafi bani mamaki shine ta
yadda mutum zai dage yace abu
kaza karyane ko kwata-kwata ba
haka bane ko rainin hankali
alhalin litattafan sa cike suke da
wadannan ruwayoyi "laa tu'addu
walaa tuhsaa". Na fiso inama dai
mutum a kashin kansa yace kawai
dai bai yarda ba akan kansa
wanda babu dama wanda ya isa
yace dole ne sai ya yarda, ya tsaya
iya nan. Yau da ace kai mai
inkarin kana da wani matsayi ne
na matakin ilimi masalan ace kai
ka tumbatsa har kakai matsayin su
Malam Maaliku da Malam Shafi'iy
ko Malam Hanbaliy to da babu
mamakin aji kayi inkarin abu farat
daya ta irin wannan yanayin,
domin a dai-dai lokacin kana kan
matsayi ne na Mujtahidin da ka iya
dangas da kansa yace ni a gurina
mas'ala kaza hukuncin kaza ne da
kaza. To amma "ma'al-asaf"
mutum bai kai irn wannan
matakin ba amma ya rika sakin
baki a fagen da bana wasan yara
ba ne, fage ne na Masana
wadanda suka tumbatsa da ilimi ta
fannoni daban-daban wanda dasu
ya kamata ya rika jingina bayan
sa, ba da kansa ba wanda ko a
cikin kewayen layinsu idan wasu
suka ji yana Magana ma akan
abinda ya shafi addinin musulunci
zasu rike baki, amma yazo yana
zage-zage da kafirta mutane.
Dukkanin irin hujjojin da muke
kawowa mukan kawo hujjojin mu
da jingina bayan mu da irin
wadannan mutanen ne wadanda
daruruwan shekarun da suka wuce
sun tumbatsa a fagen ilimi, kuma
mukan kawo litattafan da
Malaman da kukayi imani da su
ne.

Lallai mu mukan yiwa al'umma
baki dayan ta uzuri akan ta rika jin
abinda muka fada a irin matsayi
na mamaki da jin sabon abu bawai
don babu shi ba, a'a sai don abin
yanzu yazo mata, da can bata san
shi ba. Don haka akwai yiwuwar
zuciya taki karbar abin ta farat
daya nan take sai bayan mutum
abin ya shige shi daya bayan daya
yau da gobe ya bincika ya tabbatar
da abin daga baya ya zamar masa
jiki. Daga karshe nake cewa: "lau
kullifal-kullu an yatruka maa –
ya'taada tiflan naashi'an au
harimaa – la shaqqahu wa lam
yaqullahu illa – ba'ada riyadati
lisaanin thaqalaa".
Allah ya ganar da mu gaskiya ya
bamu ikon binta.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post