Da Samun da Rashin Duk na Allah ne..
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
Wataqila qarancin tawakkali ne ko kuma rashin yadda da hukuncin Allah kan sa kaga mutum ya fada cikin halin tausayi da takaici don ya rasa wani abinda yake so a rayuwarsa.
Wannan abu ya fi aukuwa cikin soyayyar samari da 'yan mata, domin wani kan rasa ransa (life) ko kuma shiga Uwa duniya bisa dogaro da cewa rayuwarsa ba ta da amfani matuqar ya rasa abinda yake so.
Tabbas babu dadi ace kun shaqu da junanku tare da sakankancewa kan cewa za ku zama abu guda a matsayin abokan zama (couple👫) na rayuwa, sannan ace an sami matsala daga baya.
Na'am, yawancin wannan matsala an fi cin karo da ita sanadin matsalar da iyaye ke haifarwa.
Muslimci ya koyar damu yadda ake neman aure shine a nemi izni daga iyayen yarinya kafin ace an fara magana da ita, amma sai ya kasance an kaucewa wannan hanya.
Ko da ace an sami matsala daga asasi ta dalilin rashin neman izni kafin fara nema, hakan ba zai zama hujja ga iyaye su bar 'ya'yansu su riqa soyayya wacce za ta kai su ga tsananin shaquwa da juna sannan su kuma suce aure tsakanin su ba zai yiwu ba. Hakan shi ke sa kaga masoya sun sami kansu cikin wani yanayi wanda ba za aso ji ba ballantana gani.
Abinda ya hau kan iyaye shine, da zarar sun ga 'yarsu ta fara soyayya da wani, to su nemi sanin wannan mutumi da kuma sanin matsayin 'yarsu. Idan sun aminta da wannan mutumi babu laifi su yi wani alqawari ko yarjejeniya tsakani ta hanyar da ta dace zuwa lokacin da su iyaye ke ganin za su iya aurar da 'yarsu. Idan ya kasance ba su aminta da mutum ba kada son abin duniya da kuma nuna rashin sanin ciwon kansu ya sa su bar yaran nan su riqa alaqa ba.
KARANTA WANNAN:-Yadda Ake gane Sallah ta karbu.
Kai/ke kuma ko da hakan ta faru a kanka/ki kar ka/ki ji cewa wannan abu zai yi sanadin fadawarka/ki cikin garari, haquri da yarda da qaddarar Ubangiji za ta magance muku komai.
Duk wani abinda ka ga ka samu ko rasa daga Allah ne, ko da kuwa an sami sanadin hakan ne ta dalilin wani.
Sau da yawa za ka so wani abu amma sharri ne gare ka, kuma sau da yawa za ka qi wani abu alhali khairi ne gare ka, Allah ne kadai ya sani, kai ba ka sani ba.
Idan hakan ta kasance sai ayi haquri da juna tare da zubar da hawayen 💧💧😭 takaici.
" FASSABRU-JAMEEL "
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~ 21st November, 2019.
Tags:
Taskar Ma'aurata