—Imam Jafar (As) yace, " Ka jarraba yan uwan ka da wadannan halaye guda biyun." 'Ikhwan' yana nufin mutanen da zaka zaba a matsayin yan uwanka, kuma makusanta daga abokanka.
—Shakka babu kayi duba garesu in suna da wadannan halaye biyu. Idan suna dashi hakan yayi daidai (Falillahil hamd), idan kuma basu dashi to, ka nesance su.
—Menene wadannan halaye biyun da Imam yake magana? Na farko shine, "Suna yin sallah a cikin lokacin ta, abin nufi akan 'cikin lokaci'na nufin da an kira Sallah din wanda wannan lokaci shine lokacin da aka umurta .
—In ba haka ba, koda lokacin ne da ya yazam dai anihin lokacin Sallah din bai fita ba, koda karshen awar fitar lokacin ne. Idan wani baiyi sallah ba to, fasiqi (azzalumi) ne."
—Hadisin yaci gaba da cewa; "Kuma su zam masu aikata kyakkyawan abu ga yan uwansu lokacin dadi ne ko lokacin wahala.
—Halayya na biyu kuma, halin zamantakewa da jama'a na farko shine kasatan tsakanin Bawa da Allah madaukakin Sarki. Na biyu kuma tsakanin bawa da sauran mutane.
—Don haka, aboki na gari shine wanda yake aikata kyakkyawan aiki ga yan uwansa lokacin dadi da wahala. Lokacin dadi da wahala yana nufin yanayin da mutum ka iya taimaka wa, ko kuma in wani na cikin matsanancin hali.
—Misali: Basu da kudin da zasu taimaki wani, amma sukan taimaka da dadadan kalamai da kwantar da hankali ko kuma da girmama wa. Aboki na gaskiya yakan taimaki dan uwansa a dukkan yanayi (Halin da ya tsinci kansa).
An dan yanko ne daga Lakcar Imam Khamenei wanda yai na Dars Kharij-Fiqh daya fadada daga hadisin Imam Sadiq (As), 11 ga watan Janairu, 2011.
Yan uwa in kunga kuskure daga gareni ne, ni dana fassara, fatan Allah (T) zai yafe min.
Dalibinku mai rauni.
Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ