#Zariamas..
•
*Tare dani Ni'imatu Muktar Daura
•
Tashin hankalin da muka tadda a Gidan Sayyid Ibrahee Zakzaky (h) a Lahdi
A daidai wannan lokacin gabda 12 na ranar 13/12/2015 sojojin Nijeriya suna gabda kewaye mu a kofar gidan Sayyid (h) a Gyallesu bayan sun kashe daruruwan Yan uwa wasu gasu cikin jininsu! Duk an kashesu saura tsiraru har takai da bana iya kuzarin kirki saboda gajiya dan tun shigowarmu da asussubahin lahdi ba mu ko huta ba. Waa musibataaa😭
A daidai kofar gidan Sayyid kuma ga Yan uwa nan wasu cikin jini wasu sun yi shahada ciki makil ba masa tsinke. Nan take kuma Malam Muktar Sahabi yana zirga zirga yana kuka yana cewa:
" *Ina wanda sukawa Allah alkawari to yau ga ranar ta zo?! Ina wanda suka sadaukar, yau ga ranar sadaukarwa, ina wanda za su bada ransu su afka su kare sojojin da isawa wajen Sayyid*........."
Ana cikin wannan yanayin sai naji wata murya na cewa Yan uwa ku taho mu tare ta wajen gidan Malam Maina ga su nan zasu mana da'ira. Ya salam! Nan take wasu suka taro wanda bamu kai goma ba muka tare makasan nan marasa imani da abinda muke iyawa. Kan kace me sun shahadantar da rabinmu saura suka tarwatsace, jini kawai nike iya gani a farfajiyar gurin, wasu yan uwa suka dake wanda bamu kai biyar ba suka tsaya kyam a karkashin ginin taransifoma muka cigaba da jefa duwatsu amma bamu iya tsaida sojojin nan ba. Kan kace me sun iske mu cikin barin wuta ba kakkaftawa, nan take muka tarwatse wasu suka koma bangaren gidan sayyid wasu kuma suka yi dayan bangaren a duke wasu da rarrafe.
.
Waa musabati!
An tsaya iya tsayawa! Haka aka wuni a tsaye kafin sun kai ga kofar gidan sai da suka kashe kowa suka kona kowa da komai!
Harbi kawai kake ji tako'ina! Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun mlm Musa
*DAGA SHAFIN MA'ASUMAH NIG NEWS UPDATES*
NA'IMATU MUKTAR DRA
Tags:
Munasabobi