Jagoranci Al'Ummar Musulmi ba Kamar Yadda Wasu Ke Dauka bane, A'a Imami Dole Yazama Zababbe Daga Allah.



╰➝Munyi imani cewa imamanci, kamar annabci ne, dole ya zam zabi ne da Allah keyi ta hanyar manzonsa, ko kuma zabi ta hanyar wani Imami.

╰➝Idan muka duba daga wannan matsayar, Imamanci  kamar annabci ne. Ba daidai bane ga mutane su ke shawarwari akanshi (Imami) domin shi wanda Allah ne ya zaba musu, ya zama mai saita su kuma shugabansu.

╰➝Sabila da haka basu ne zasu zabe shi ba, wanda yake da ikon ayyana Imami ko nuna shi dole ya zam zababbe daga Allah (T).

╰➝Munyi imani cewa; Manzon Allah (S) bai bar duniya ba saida ya bayyana wanda zai wakilceshi yayi jagorancin musulmi (Khalifa) don haka ne ya zabi dan uwansa 'Ali Dan Abi Talib a matsayin Shugaban Mu'minai'.

╰➝Mai kare abinda aka saukar ga wannan Manzo din, kuma shugaban dukkan mutane. Manzon Allah ya wajabta wa kowa yin rantsuwa don yarda da Imamancinsa hakan ya faru a wani wuri da ake kira Ghadir Khum.

KARANTA WANNAN:-Daga Annabi muka koyi yiwa Azzalumai Mummuniyar Addu'ah!!


╰➝Kuma yace a wannan lokacin: Yaku Mu'minai! Duk wanda ya yarda ni shugabansa ne, to ya riki Ali shugabansa. Ya Allah! Kaso Wanda yaso Ali, ka taimaki wanda ya taike shi, kuma ka hana wanda ya hana ma Ali, Allah kasa gaskiya ta kasance koda yaushe tare dashi.

╰➝Waje na farko da Manzon Allah ya fara bayyana khalifanci shine lokacin daya fara tara makusantan sa da danginsa yace dasu:

╰➝Shi (Ali) dan uwana ne, kuma wasiyyi na sannan khalifa na. Ya zama wajibi gareku kuji daga gareshi sannan kuyi masa biyayya. A lokacin da Manzon Allah (S) ya fadi wannan, 'Ali bai gama girma ba'. Manzon Allah yayi magana akan haka lokuta da dama:

╰➝Ya Ali! Kai a wajena kamar Haruna ne da Musa; saidai ni babu annabi baya na. A wasu ruwayoyin an bayyana shugabancin Ali akan mutane, kamar yadda yazo a cikin Alqurani mai girma kamar haka:

╰➝"Abokin Allah ne kadai da Manzon sa, da mu'minai wanda suke sallah, kuma suke bada zakka alhali suna ruku'u. Saratul Maa'ida, Surah ta 5, aya ta 55. Karshen ayar nan ta sauka ne kan Imam Ali (As).

╰➝Ali ne yake ruku'u ya bada zoben sa ga mabukaci alhali yana ruku'u cikin sallah. A gaskiya bazamu iya kawo dukkan nin ruwayo da sukai magana akan Ali ba domin abubuwa ne dasuke ba iyaka.

╰➝Imam Ali shima ya bayyana imamancin Hasan da Husaini cikin jama'a da kuma Imamancin dansa Ali Zainul Abideen, kuma ko wanne imami daya biyo baya, an zabe shi ne ta hanyar Imami wanda yake jagoranci a lokacin kafin shi yazo.

╰➝Muna kara godia ga Allah madaukakin sarki daya ganar damu wannan hanya ta sa ta gaskia, har muka san imaman zamanin mu.

╰ー Alhamdulillah bi hazan ni'ima, ni'imar Imamanciー╯

Yan Uwa barka da Juma'a fatan zamuyi Sallah cikin koshin lafiya.

      ᕙ(⇀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ↼)ᕗ

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post