Tsakanin Yan Nigeria da Buhari
✿✿✿ ✿✿✿✿✿ ✿✿✿
```ĎĂĜĂ MĂŜ'ŨĎ ĎĂŇ MĂŜĂŇĨ ŜĤĨŇҚĂҒĨ
✿✿✿✿✿✿✿ ✿✿✿ ✿
Ingiza Mai Kantu Ruwa
Wannan furucin daxaxxen karin magana ne a bakunan Hausawa, a wasu sassa na qasar Hausa akan ce da shi, ‘tura wawa daji’. Kantu wani dogon sunqin gishiri ne da ake yi a da. Ga al’ada gishiri da ruwa ba abokan hira ba ne. Da an sa gishiri a ruwa zai narke a rasa inda yake sai dai in an sha ruwan a ji samatarsa. Ashe komai girman kantun gishiri idan aka ingiza mai shi cikin kogi an gama da labarin kantun sai dai shi mai kantun a je a cece shi in bai iya ruwa ba. Don haka, ingiza mai kantu ruwa na nufin a sa mutum ya yi abin da zai ba shi ruwa ya cutu ga jiki ko ga suna ko ga martaba da dai makamantansu. Idan aka bi fassarar masu kiran sa, tura wawa daji, ana nufin a sa wawa ya yi abin da ba zai iya fitar da kansa ba sai an fitar da shi. Ga xan misali domin a Tantance irin yadda mutanen nageria sukayiwa general Muhammad buhari:
An ce, wai wata rana wani Sanqira na yi wa sarkinsa kirari aka je za a qetare kogi babu jirgi ga ruwa da zurfi kuma sarki bai iya ruwa ba. Da sanqira ya hau bakinsa yana cewa:
“Kai ake tsoro ka wuce tsoro
wane mutum bale wani dabba
ko ruwa suna tsoronka.
Yau ga kogi bisa kogi
sai mun ga mai shirin kauce wani.
taka da gaskiya mai nasara
wallahi ko cikin ruwa kuna gwada iko”.
Sanqira ya san da Sarkinsa bai iya ruwa ba, amma ya tsima shi da kirari. Daga cikin kirari ya yi ingiza mai kantu ruwa, domin ya ce, kowanensu kogi ne babu damar xaya ya ratse wa xaya. Da sabbene ya }asura sai ya yi alqafura (sukan tsari) cikin kogi da alkyabba da rawani da qyar aka tsamo tsama tsama. Akums lura Irin dabarar da maharba ke yi wajen harbin birai (Bika) su juya kibiyar su nasa kyarmon a ciki su yi ta kirari, su zage su harbi biri ya carve (sarve) kibiyar, shi ma sai ya nasa a ciki wai ya yi yadda aka yi mass. Da ya nasa sai ta shige a cikinsa sai mutuwa. Wayyo haka yan Nageria suka tayiwa Baba buhari gashi *RUWA YACI GWANI NAGERIA TARIKICE* AGASKIYA YAN NAGERIA BAKUWA BABA BUHARI ADALBA, AMMA KUMA ZAKIJI AJIKIN KU KAMAR YADDA YAKEJI AJIKIN SA DOMIN JIKI MAGAYI NE.
.
Naku Mas'udu Dan masani Shinkafi
_*Muhammad Ibraheem one touch*_
Mdanmasaniskff@gmail.com