Imam Ali (as) a yakin khaibara


-Khaibara wani gari ne daga garuruwan Yahudawa dake makwabtaka da Madina.
-Garin na bisan dutse ne, an kewaye shi da ganuwar dutse, wanda ‘yan garin ke
zaton za ta iya kare su daga takubban masu jihadin da ke samun taimakon Allah.

-Yahudawan Khaibara suna da Dabi’un sauran Yahudawa, rudin kai ya mamaye su, don haka Khaibara ta kasance wata cibiya ta kullawa musulmi
makirci.

-A ganuwar Khaibara akwai mayaki kimanin dubu goma, kullum suna fita sahu-sahu don yin atisaye, har suna yin izgili da irin karfin da Musulmi ke da shi
suna masu cewa: “Mahammadu ne zai yake mu? Ko kusa!”

-Manzon Alah (S) ya hada rundunarsa da
azamarsa, ya kuma boye madosarsa. Ya bi hanyoyin da zai sa duk wani yunkurinsa ya zama cikin sirri, ya dogara da wasu masu nuna hanya.

-Don haka Yahudawa ba su sami wani labari ba sai bayan da Musulmi suka sauka a fagensu da daddare.
-Lokacin da suka sami labarin isowar Musulmi sai shugabanninsu da masu fada aji a cikin su suka yi taro don tsara hanyar da za su fitowa al’amarin da hana kai hari ganuwarsu.

-Hari ya fara ne yayin da Manzo ya aiki Abubakar “sai ya dawo ba tare da ya sami nasara alhali ya yi iya kokarinsa .

-Malam Tabari ya ce: “Manzo Allah (S) ya bayar da tuta ga Umar dan Khaddabi, ya kuma hada shi da wasu mutane, suka je suka hadu da mutanen Khaibara, sai Umar da mutanen shi suka kasa suka dawo wajen Manzon
Allah (S) alhali mutanen da suka tafi da shi suna ragontar da shi shi kuma yana ragontar da su (wato kowa na razana dan’uwansa).

-Sai Manzo (S) yace: “Lallai zan bayar da tutar yaki gobe ga
wani mutum da ke son Allah da Manzonsa kuma Allah da Manzonsa ke sonsa” .

-A wata ruwaya ta Ibni Hisham, Manzo ya kara da cewa: “Allah zai buda a
hannunsa, shi ba mai gudu ba ne” .
-Da aka wayi gari, da ma Abubakar da Umar na ta sa rai ko su ne za a ba su wannan tuta, amma sai Manzo (S) ya kira Ali Sai ya ce masa: “Karbi wannan tuta ka tafi da ita har
sai Allah ya bayar da nasara ta hannunka”.

-Sai Imam Ali (a.s) ya karbi tutar ya yunkura tare da wasu Musulmi, ya gabaci ganuwar Khaibara, sai wani
shugaban Yahudawa ya fito tare da wasu mutane daga jama’arsa don ya yaki Imam Ali (as) sai shi kuma Imam Ali ya gaggauta sare shi a kai har sai da wadanda ke rundunar suka ji karar saran da aka yi masa “.

-Da haka Imam Ali (as) ya bude kofar, duk wani kuzarin Yahudawan Khaibara ya wargaje daga nan, kuma
Allah Ya ba Manzonsa nasara babba, aka watsa
waccan runduna mai karfi.
Don karin Bayani sai aduba:

-Siratul-Nabwiyyah na Dahlan, juzu’i na 2, shafi na 6 da 7.

-Mustarak al-Sahihain, juzu’i na 2, shafi na 32, daga Sufyan al-Thauri; haka nan Khatib al-
Bagadadi ya ruwaito shi a cikin Tarikh Bagadad, juzu’i na 13, shafi na 19.

-Ibn Hisham, cikin al-Siratul-Nabawiyyah, juzu’i na 3, shafi na 349, bugun Darulu-Ihya’il-Turath al-Arabi, Beruit.

-Tabari cikin Tarikhul-Umamu wal-Muluk, juzu’i na
2, shafi na 300.
-Tarihin Tabari, juzu’i na 2, shafi na 300;
-Muhammad Jiddah Nguru
08069306985.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Imami Ali asw shene kadai Allah yazaba saboda shine annabi ya mankuntu maulak
    um fahaza aliyu maulakum

    ReplyDelete
Previous Post Next Post