TAKAITACCEN TARIHIN SHAHID SAYYID AHMAD
An haifi Sayyid Ahmad a ranar Asabar 13th October 1990, wanda yai dai-dai da 24 ga Rabi'ul Auwal 1411. A unguwar kwarbai dake cikin Birnin Zazzau a jihar Kadunan tarayyar Najeriya.
Sunan sa Sayyid Ahmad Ibrahim. Yana da Laqubba kadan daka ciki, jama'a na kiran sa *Commander*, Iyayan sa kuma da *Fa'iz* wanda na sani daga Gidan su.
NASABARSA
Nasabarsa ta wajan Mahaifinsa: Sayyid Ahmad, shine dan Allamah Ibrahim Zakzaky, shi kuma dan Malam Yaqoub shi kuma dan Malam Aliy dan Malam Muhammad Tajuddin dan Liman Husaini. Shi liman Husaini wani bawan Allah ne kuma Babban malami da yake limanci a wani Masallaci a lokacin. Malam Muhammad Tajuddin yazo birnin Zariya ne daga Sokoto a cikin tawagar Amir na Zariya. Wato lokacin da Shaikh Usman dan Fodiyo (RA) ya na da Malam Musa a matsayin Amir na lardin Zazzau sai ya hada shi da Malam Muhammad Tajuddin a matsayin mai bashi shawara, da kuma mai taimaka masa wajan tafi da harkokin jama'a akan tsarin Musulunci.
Nasabar sa ta wajan Mahaifiyarsa kuwa, Sayyid Ahmad dan Malama Zeenatuddeen ita kuma sunan mahaifinta Ibrahim sunan mahaifin shi Muhammad Auwal. Sunan mahaifiyarta Maryam, ita mayaryam dinnan jikanyar wani shehin malami ne dake Illoron Imam Akayede. Sunan mahaifin mamanta Malam Abdullahi.
KARATUN SA.
Ya fara da karatun gida ne a bangaran karatun Al-Qur'ani da karatukan Fiqihu da fannin Ibadat da Ma'amalat da kuma fannoni dabam-dabam da ake karantawa a zaurukan karatu a cikin Birnin Zariya, wadannan duk a gun mahaifin sa ya karanta su a gida.
Ya yi karatunsa na primary a Buk International School dake daura da filin koyan tuqin Jirgin sama na Aviation dake Zaria, daga shekarar 1996 zuwa 2002
Yayi makarantar Thybow International School Zaria daga 2002 zuwa 2004, daga nan yabari ya koma Zaria Academy daga 2005 zuwa 2007 sai yabar Zaria academy yakoma Holemark har akayi masa double promotion yashiga SS2 maimakon yashiga SS1. Bayan nan yagama Secondary School A 2009, Amma baisamu wucewa makaranta ba sai a 2011.
Ya yi amfani da wannan damar wajan fadada bincike a kan wasu fannoni na karatun sa. A lokaci guda kuma ya sami dama sosai wajan taimakon mahaifin Sa a kan ayyuka na yauda kullum da mahaifin sa Shaikh Ibrahim Zakzaky (h) ya saba gudanarwa domin taimakon Al-umma, kamar tafiye-tafiyen sa da ayyukan gine-ginen cibiyoyin addini dama wasu ayyukan dabam.
Yasami nasarar wucewa China ne A shekarar 2011, Inda yayi karatunsa na Chemical Engineering wanda a shekarar sa ta qarshe dazai kammala, bayan dawowar sa hutu ne, sojojin gwamnatin ebele jonathan "yan inada kisa suka aiwatar da kisan kiyashi akan masu muzaharar qudus ta duniya a Zaria, wacce ake yi duk shekara, dan nuna tausawa ga al'ummar Palastinawar da haramtacciyar qasar Isra'el keyiwa kisan gilla fiye da shekaru 60+ wanda duniya tai shiru akai. Sayyid Ahmad yana cikin mutum 34 da sojojin suka kashe, ciki har da kannan sa biyu Sayyid Hameed da Sayyid Mahmud.
Sayyid Ahmad ya sami cikakkiyar tarbiyya daga mahaifinsa, dan haka ya haifar da ayyuka na musamman da suka zama abin koyi ga yan baya. Tun yana yaro ya yi aiki kafada da kafada fanin tsaro na Harisawan Harkar Musulunci sakamakon cigaban tunanin sa yasa ya kafa rundunar Muassasatu Sayyid Abul Fadalul Abbas (A.S) wannan rundunar bayan kafuwar ta, ta haifar da rassa na fannonin ayyukanta a ciki da wajen harka zuwa sassa dadan-daban.
Sayyid Ahmad Yayi shahada a shekarar 2014/25/July. Lokacin yana da shekaru 25 a duniya sojojin Nijeria sum masa kisan irin na gabar jahiliyyar qarnin farko kafin zuwan Manzon Allah (S.A.W.W) ta yanda suka harbi duk wata gaba mafi mushimmanci a jikin sa da harsashi, da dan Adam zai iya dogara da ita dan samun damar motsawa, sun kashe shi tare da dan uwan sa Sayyid Hameed Ibrahim Zakzaky (H) bayan kamun da sukai masu alokacin muzaharar ta Qudus.
Amincin Allah ya tabba a gareka ya Shahid Ahmad ranar haihuwar ka, da ranar shahadar ka, da ranar da zaka dawo rayayye domin daukar fansar jinin Kakan ka, Imam Husaini (A.S).

Karami kuma autan gidan Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) Shahid Sayyid Humaid
Tags:
Munasabobi