-Muhammad Jiddah Nguru
08069306985
-Duk fadin Nijeriya Babu Mai gaskiya sai kai sai Wanda kake so, Babu Wanda ya iya komai sai Kai sai Wanda kake so, Babu Mai baka shawara sai Wanda kake so Koda kuwa dakiki ne Jahili Wanda bai San komai ba,
-Duk abinda kake so shi za ayi dole Koda kuwa ba zai bada ma'ana da natija ba, dai-dai din ka shine dai-dai Koda kuwa ba dai-dai bane, ganganci da kuskuren ka dai-dai ne koda kuwa za a kashe Mata da Yara, Sojoji da 'Yan sanda.
-Tun daga farkon Mulkin ka Masoyanka na hakika sun nuna maka akwai gyara a tafiyarka, Amma sai ka nuna musu kafi Dan dako sanin Tasha, Yanzu dai ga Najeriyar ga ka, ga Kuma Talakawan da ka yiwa alkawarin Samar musu da komai.
-Ka sanya Malaman Fada a gaba wadanda Shinkafa da Taliya take Hana su Fadar gaskiya, Wadanda kudi yake sanya su halatta haramun da Kuma halatta zubar da jinin raunana marasa makami, wadanda suke cewa duk Wanda ya Fadi laifinka ya Sabawa Allah Ta'ala, wadanda suke cewa duk Wanda ka kashe ka kashe banza Allah Ta'ala ma ba zai yi hukuncin akai ba saboda jahadi kayi.
-Wadannan bunch of idiots din ne, ka fi yarda da aminta dasu Akan kowa, sune Kuma suke Hana ka sauraron kowa Akan dukkan wahalar da Talakawan Nigeria wadanda suka kasa suka raka suka jira domin ganin ka zama Shugaban Kasa.
-Ko ka manta lokacin da ka tambayi kudin taliya aka ce maka 100 naira ka fashe da kuka.
-Yanzu kam gwamnatinku ta shahara Wajen Shirgawa Talakawa karya, daga kan Oga kwata-kwata, Ministocinsa, Gwamnoni, Manyan Sojojin, Shugabannin 'Yan Sanda, Sarakuna da Malaman Fada Wadanda aka Basu Kwangilar kafirtawa tare da halatta kashe dukkan Wanda Yace Gwamnatin ka ta gaza, dukkansu da karya suke alfahari.
-Tun hawanka karagar Mulki Wanne abun arziki Gwamnatin ka ta tsinanawa Talakawa zuwa Yau.?
-Mu dai Mun ga kuna kashe Mutane Marasa Makami, kun kashe Mata da Yara Marasa Makami, Barayin Shanu da Kidnappers sun Kara Karfi, idan Kuma akwai wani abinda Gwamnatin Buhari ta yiwa Talakawan Nigeria ba Wannan ba a fada Mana..
-Ko kun San dalilin da Yasa komai ya damalmale Muku Kuka kasa tsinana komai a Mulkin ku? Idan baku sani ba to ku sani ta'addancin da kuka sanya sojoji suka yi a ranar Asabar 12 ga Disamba, 2015, wanda kuka sanya rundunar sojin Nijeriya ta aiwatar da abin da za a fi bayyana shi da kisan kiyashi a kan fararen hula da ba su dauke da Makami, wato ‘yan uwa Musulmi Almajiran Malam Ibrahim Zakzaky (H) a garin Zariya ta jahar Kaduna.
-Wallah summa tallahi Irin Mummunan ta’addancin da sojojin nan suka yi shine ya sanya komai naku ya tabarbare, duk abinda kuka sanya agaba na alkhairi baya Yuwuwa
-Sannan kuma Sanannen abu ne ga kusan kowa da kowa, cewa cigaba da tsare Sheik Zakzaky yana daya Daga cikin Abubuwan da suke kara dagula al'amarin gwamnatinku, Kun kashe Masa 'Yayansa uku da Mabiyansa sama da dubu 1000+, kun rushe Masa gidansa, kun kona yayarsa da ranta, kun rushe Masa gidansa da ya gina, kun rushe duk wani abu da yake da dangantaka da Harka Islamiyya, kun harbe shi da harsashi mai guba, Wannan Wanne irin zalunci ne haka?
-Tayaya Allah zai bar Wannan zaluncin hakanan?
-Mafita daya ce ku saki Malam Zakzaky da Mai dakinsa, da Dukkan 'Yan uwan da kuke tsare da su.
-Muhammad Jiddah Nguru
08069306985
Tags:
Tunatarwa