GAEGADI:-Idan muka so Abunda Allah da Manzon sa suke ki, Kuma muka girmama Abunda Allah da Manzon sa Qasqantacce..!!!


Daga Hudubobin Imam Aliyu (As).

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KHUDUBARSA KAN BIN SUNNAR MANZON ALLAH (S.A.W.W)

" Ku yi koyi da Manzon ku (S.A.W W) tsarkakekke mai tsarki,a tare da shi akwai kyakkyawan abin koyi ga ma su bi, kuma akwai kwanciyar hankali ga mai neman kwanciyar hankali. Ma fi soyuwa a gurin Allah shine wanda ya bi (koyarwar) Manzonsa (S.A.W.W).

Bai dauki wannan duniya a bakin komai ba. A dukkan duniyar nan shine ya fi kowa yashin qoshi na ciki (na rashin cin abinci a qoshi). An miqa masa duniyar amma ya qi yarda ya karbe ta. Ya tsani duk wani abu wanda Allah ba ya so, idan Allah ya qasqantar da abu shi ma ya qasqantar da shi, idan kuma ba ya ganin girman abu to shi ma ba ya ganin girman abin.

KARANTA WANNAN:-Kada Kayi farin Ciki da Samun Duniya ta Hanyar Sabawa Allah !!!


Idan har muka so abinda Allah da Manzonsa suke qi ko kuma girmama abinda Allah da Manzonsa suke ganin sa qasqantacce, to, wannan ya isa ya nesanta mu daga Ubangiji da kuma wuce iyaka da shisshigi ga dokokin Allah.

Manzon Allah (S.A.W.W) ya kasance mai cin abinci alhali yana zaune a qasa, kuma ya kan gyara takalminsa da kansa. Ya kan dinke rigarsa idan ta yage da hannunsa, kuma ya kan hau kan Jaki wanda babu sirdi.

Idan ya ga labulen daki da zane-zane a jiki a qofar dakinsa ya kan ce da daya (1) daga cikin matansa,

" KE WANCE KI 'DAUKE SHI DAGA GABANA, DOMIN KUWA GANINSA YAKAN SA A TUNA DA KYALLALIN DUNIYA ".

Don haka ya cire zuciyarsa daga son duniyar nan, ya fitar da sonta daga zuciyarsa. Ya kasance yana so a boye qyalqyalinta daga idonsa. Saboda haka ya kamata mutum ya yi koyi da Shi (S.A W W), Idan ba haka ba ba zai tsira daga tabewa ba.

Babu shakka, Allah (T) ya sa Muhammad (S.A.W.W) alama ta ranar sakamako, mai isar da bushara da Aljannah, kuma mai gargadi da azaba. Ya bar wannan duniya yana mai jin yunwa, ya shiga daya duniyar a cikin aminci. Ubangiji ya yi mana baiwa da Manzonsa a matsayin wanda ya gabace mu, abin koyi kuma shugaban da za mu bi  ."

(NAHJUL-BALAGHA, SH:323)

Tare da Ado Isah Guda

~ 21st November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post