👆🏽------------------------- 👇🏽
--Inji jagoran gaskiya [Sayyid Ibrahim Alzakzaky]
"Wato a taqaice abin da nake cewa, ‘destiny’ din al’ummar nan yana
hannunmu ne, kuma ba zai taba yiwuwa kana tunanin wai gyaran Allah
kawai a wayi gari a ga an gyaru ba. Gyaran Allah shi ne me kake so
Allah ya yi maka? Ya aiko da wane Annabi? Ya riga ya aiko.
Ko ya
sauqar da wane Alqur’ani? Ya riga ya sauqar.
Ba abin da zai yi maka
illa ga saqon nan, in za ka bi ka bi, in ba za ka bi ba kuma ya rage maka,
a hadu a ranar hisabi.
To, ni yanzu na ga kamar mutane sun yi saranda ga halin da suka
sami kansu ne, ana jiran kawai a yi ta tafiya haka nan. Kuma kullum
abubuwa sai qara tabarbarewa suke yi da lalacewa. In ka ga wannan
nau’in lalacewa ya fito, sai ka ga na kashegari ya fi shi muni. Sai ka ga
wani ya sake kunno kai, shi kuma ya fi na jiya, kuma haka ake ta tafiya
ana dai zaune haka nan kawai.
Abin da nake cewa in wadansu mutane in za su zama ma’azurai,
musulmi ba shi da uzuri, don shi tsiransa na hannunsa. Shi Allah Ta’ala
ya fifita da shiriya, sai ya ajiye waje guda. Ba wata mafita gare mu illa
mu san cewa mune da kanmu za mu yi, ba kuma jiran wani za mu yi ba.
Mune da kanmu, kuma al’marin yana hannunmu ne!�
👇🏽------------------------👇🏽
Ma'asumah Nigeria 🇳🇬 News Update, [Filin jagoran gaskiya]
Wakilinmu:
👇🏽
Mahadi Tukur Almizan