➝Manzon Allah (S) yana cewa; "Hakika, Allah madaukakin sarki yace, 'Ban halicci wani bawa daga cikin bayina nafi sonsa kamar bawa wanda yayi imani dani ba kuma yake min biyayya"
➝Manzon Allah mai tsira da aminci ya kara fadi a wata ruwayar cewa; "Bawa mai imani shi yafi soyuwa a wajen Allah (T) fiye da mala'iku mafi kusanci gareshi."
➝Imam Sadiq (As) yana cewa; "Muminai su suka fi tsarki, fiye da dakin Ka'aba"
➝Daga Manzon Allah (S) hallau yake cewa; "Jinin mu'minai iri daya ne, kuma hannayen su guda ne akan wasu. Mutum mafi rauni daga cikinsu kums su kan kara mishi kaimi (karfi) da taimakonsu."
DOMIN KASANCEWA CIKIN MU'MINIAI YANA DA KYAU KASAN WANENE MU'MINI, DOMIN KAIMA KA KASANCE DAGA CIKIN MAFI SOYUWA A WURIN ALLAH
➝Manzon Allah (S) yake fada da bakinsa mai albarka,"Mu'mini shine mutumin da mutane suka aminta dashi da jininsu da kuma dukiyoyinsu"
➝A wani hadisin kuma Imam Ali (As) yace; " Mu'mini shine wanda yake mutum hakuri, a fagen neman 'yanci kuma marar tsoro ne shi."
➝Imam (As) ya kara cewa; "Mu'mini shine wanda yake tsarkakakke tun daga tushensa."
╰Allah ka kara mana tsoronka, ka ma karemu da kariyarka, ka kuma azurta mu da kasance koda yaushe masu biyayya a gareka alfarmar masoyinka Manzon Allah (S). Ya Allah ka kwato mana jagoranmu a hannun azzalumai cikin izzah da nisan kwana╯
ᕙ(⇀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ↼)ᕗ