@ Ma'asumah Nigerian News Update @, tare da Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ.
-hakika, matasanmu suna tafka babban kuskure, suna wasa da aure wanda shine tushen al'umma sunnar ma'aiki mai karfi. Ta hanyar aure ne ake hayayya far da al'umma har su zam ababen alfaharin Manzon Allah (S).
-Maimakon neman samar da iyali na gari, yanzun mun dauki wata hanya wacce ba mafita mai kyau bace garemu da al'umma baki daya ba, hanyar itace; wai ala dole mutum saiya auri farar mace.
-Eh, ba matsala bane don kana son auren farar mace, amma ka tabbata ta hada abubuwan da bazaka zo daga baya kana dana sani ba, ma'ana ma'abociya addini, mai nasaba, kamala da tatbiyya.
-Matukar zamu kiyaye wadannan, zai zama hakan yana kyau, amma yanzun mun daukar wa kanmu buri da shirme irin na Aaama din mutane, waimu 'Farar Mace Ko Mayya Ce' wa iyazu billah. Ko kodai tutuyit da muke addini muke na karya ne.
-Kada fa muzam mutanen da Manzon Allah zaiyi kaico damu gobe kiyam, sabila da mun tara yara amma bamu saka su kan hanyar addini ba. Domin sai an sami uwa ta gari, kana zata maida 'ya'yanka na gari ta hanyar basu tarbiyya da tasha daga iyayenta.
-Don haka yana da kyau mubar duban kyawun fiska, mu maida akalarmu ga duban kyawyn hali da zuciya, mu nemi masoya Allah da Manzonsa (S) wanda suka zam hadafinsu addini ne ba rudun duniya da kyale-kyalen cikinta ba.
-Yar Nasiha ce fatan zamu gyara domin guje wa halakar da kanmu da iyalinmu. Wasallallahu ala Muhammad wa alihid daahireen.
Tags:
Tunatarwa