Dukkan Macce nada Abokin sirri Wanda Bata Tsoron Bayyanar Masa Abunda Ke damun ta..!!

Karanta Kuma kayi shere zuwa ga Abokkanka Mata da maza..

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KU KASANCE MA SU RIQE SIRRIN JUNA


Riqe sirri abu ne mai matuqar muhimmanci wanda ke faranta zuciyar wanda aka riqewa, sannan kuma yakan cutar da wanda aka bayyayar da sirrinsa ga wanda bai so ya sani ba.


Abokin sirri amini ne wanda ba a tsoron bayyanar masa da dukkan wani abinda ake son aikatawa ko kuma damuwar da ke damun mutum.


Uwa ita ce mafi kusanci ga dukkan abinda ta haifa, kuma mafi nuna soyayya da tausayi gare shi, amma hakan bai hana 'yarta (daughter) ta boye mata wani sirrin ta ba, kuma ta bayyanar shi ga saurayinta ko mijinta, domin ta fi aminta da shi wajen bayyanar masa sirrin dukkan abinda ke damun ta ba tare da jin wani tsoro ko fargaba ba.


Abinda ya kamata ga dukkan namiji shine, ya kasance mai riqe mata sirrinta fiye da yadda yake bada kariya da tattalin dukiyarsa, tare da amintar da ita kan amintar da tayi masa.


Zai kasance cin amana ka riqa bayyanar da sirrin wanda ya aminta da kai, kuma bai yarda ya bayyanar da sirrinsa ga wani koma bayan ka ba.


Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da Ado Isah Guda.


      08126385470


~ 19th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post