Da'irar Shinkafi Bazamu taba mancewa Da ranar Wata Al'hamis 6 ga watan ramadan Wadda tayi dai-dai da 1-jun-2017, Ranar data zamo mana ranar kuka da yoyon ruwan hawaye, Ranar da kowa kagani cikin wani Yanayi Na rashin lafiya, Ranar Da Mai rabawa ta raba masoyi da masoya, ta raba uwaye da dan su, ta raba kanne da wansu, ta raba Aboki da Abbokkan sa dss.
!
Abdussamad ya zamo jarumi gwarzon matashi Wanda da'irar shinkafi bazata taba mantawa da babban rashin shiba, domin takai Wakilin yan uwa Na da'irar Shinkafi MLM QASIM SHEHU SHINKAFI yana tunatar da matasa akan koyi da rayuwar MARGYAYI ABDUSSAMAD a ziyarar da matasa suka kaimasa ta barka da Sallah a gidan shi.
Na zamo duk nikkaranta wannan magana ta Amirul-muminin Aliy (as) sai nayi kuka inkuma tuno da rayuwar Abdussamad da kwadayin inama zansamu kamar tasa, " Amirul - Muminin Ali bin Abi Ɗalib (as) ya faɗa a cikin huɗubarsa ta (64) a nahjul balagha inda yake cewa : ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah, ku yi gaggawan gabatar da ayyukanku na alheri kafin saukan ajalinku, ku sayi abin da zai wanzu gareku da abin da zai gushe muku wata rana, ku yi tanadin guzuri domin tafiyar da babu makawa a cikinta - guzurin barin duniya shi ne tsoron Allah ta’ala ( ta hanyar kiyaye iyakokinsa) – gata ta matso tazo kusa, ku yi tanadi domin zuwan mutuwar da ta kusanceku har tayi muku inuwa kamar lema, ku kasance kamar mutanen da a kayi musu tsawa suka faɗaka, kuma suka san cewa gidan duniya ba gida ce ba gare su, sai suka nemi musanyenta da gidan lahira, domin Allah subhanahu bai halicceku don wargi ba, kuma bai barku haka nan sasakai ba, babu abin da ke tsakanin ɗayanku bayan ya mutum face aljannah ko wuta..Allah ya Datar damu da Aljannar don Darajar ma'asumai sha hudu.
.
A fagen biyayya yaro ne Mai tsabar biyayya ga mahaifansa Wanda hartakai idan yana kusa da mahaifansa suna masa magana kansa a sunkuye yake domin yanajin nauyin dago idanuwansa su hadu da nasu, yakan bar komai nasa don ya faranta musu, banmanta gab da rasuwar sa bayan ya samu sakon gayyata Na zaman media da za'ayi yakirani tare da nuna farincikinsa akan zaman dokuma sanar Dani insha Allah dashi za'ayi zaman sai gashi ya shirya amma baisamu halattaba saboda umurtashi da wani aiki da mahaifanshi sukayi, bama mahaifansa kadai ba hatta yan'uwa da mutanen gari sunsan alkunyarshi da kamun kanshi gashi da yawan murmushi akowane hali yasamu kansa ga tausayi domin kannensa Na fadin tausayinsa harfadin suke ko sunyi masa laifi baicika dukansu ba sai dai nasiha..
.
Hakika Ni nake cikin maraici domin shi ne mutumin daya.sadani da hasken idaniyata, ta dalilinsa Na Fara ganin Sayeed (h), Nasha wahalhalun datakai hatta yan uwana suka gujeni da tsanata akan harkannan da Kora..Shi ne mutun Wanda ya taimakeni ya nunaman mahaifinsa suka bani makwanci da shawarwari harzuwa inda ake yanzu.
.
KO yaushe kokarinsa yazaiyi yasamaman cigaba a rayuwata domin ba'ayi wata uku ba yakirani akan wani Al'amari Wanda yakeganin cigabane agareni nace masa yayi hakuri sai Na waiwayeshi, Allahu Akbar Allah yajikan ka Abdussamad ya haskaka makwancin ka ya sadaka da shaheededan qudus.
.
Kacika Dan uwa tunda ka tarbiyantu da koyarwar su sayyed (H) hartakai da kasamu shaida da wakilan Alama sayeed Zakzaky (h) Na garuruwa mabanbanta a zaman da kayi dasu Na Dan kankanen lokaci, Ban mantawa abundance wakilin yan uwa na shinkafi Mlm qaseem shehu shinkafi ya rubuta a shafinsa Na Whatsapp kwana 2 da rasuwarka inda Mlm yafara da yabonka tare da shaidar ka ga abunda Mlm yake cewa:
_"Bisa hakika 'yan uwa na shinkafi sun kadu matuka da wannan babban rashi na rasuwar bagatatan da wannan gwarzon saurayi mai natsuwa mutumin kirki yayi a jiya alhamis._
_*DAGA NAN SAI SHAIDAR MLM AMINU BODINGA DAYAYIWA MAMACIN DUK ACIKIN RUBUTUN DA MALAM YARUBUTA*_
Cikin wadanda suka halarci jana'izarsa akwai wakilin 'yan uwa na Bodinga Malam Aminu Atiku ga abunda yake cewa "Jiya bayan na samu wannan mugun labari sai na kira mahaifiyata a gida na shaida ai kuwa nan take gidan ya barke da kuka, saboda dan zaman da yayi damu to mun shaidi cewa yaron kirki ne da duk ma'anar kirki, kai Malam abunda kawai zance Allah ya gafartawa Abdussamad".
.
*MLM SAYYADI AHMAD WAKILIN YAN UWA NA GWARANYO*
.
Shima wakilin 'yan uwa na gwaranyo Malam Sayyadi Ahmad ga abunda yake cewa jim kadan da kammala jana'iza "Abdussamad kam ai kowa ya sanshi to tabbas zai shaideshi da kamun kai da mutunci da biyayya da kuma kawaici, Allah ya gafarta mashi"
*MLM SANI HAKIMI WAKILIN YAN UWA NA JEGA*
.
Shi kuma wakilin 'yan uwa na jega Malam Sani Hakimi wanda ke zaune tare da mamacin a gari guda kafin wafatinsa, ga abunda yake cewa yayin da yake ta'aziya "Rashin Abdussamad kam lalle ba karamar hasara bace yaro natsattse mai hankali hakuri da sanin ya kamata, ka duba ka gani cikin yaran dake garin nan shi kadaine ke zuwa karatu a kowace rana. Kai Allah ya karbi uzurinsa ya sadashi da Abu Abdullah(as)
.
Muna rokon Allah ya karbi shaidar muminai akan Abdussamad ya yafe kurakuransa ya sanyashi a ceton manzo da iyalan gidansa.
Kadan kenan daga cikin shidun da margyayi ya samu Ubangiji Allah (t) ya karbi addu'o'in da mukayi da Wanda za'ayi ya haskaka kabarin margyayi da sauran yan uwa musulmi baki daya don darajar Manzon Allah (s) da ahalinsa.
.
_*Mas'udu Dan masani Shinkafi 08149993999*_
Tags:
Munasabobi