Da bawa zai san alherin dake cikin neman ilimi to, da ya maida rayuwarsa baki daya a hanyar makaranta!!!




Kamar yadda muka sani ne, neman ilimi wajib ne ga dukkan musulmi, domin ibada bata karbuwa saida sanin ilimin yin ibada din.

Yazo a ruwaya cewa; Muhammad Ibn Jafar Ibn Muhammad ya ruwaito daga mahaifinsa, shi kuma daga kakan sa cewa yaji Manzon Allah (S) yace:

"Mai neman ilimi daga cikin mutane jahilai, kamar rayayye ne a cikin matattu. Kuma dukkan halittun Allah (T), har su kifi, dabbobin daji dasu shanu baza su gusheba  suna roka ma mai neman ilimi gafara.

Hakika, hanyar kara kusanci ne tsakanin bawa da Allah, madaukakin sarki. Shi neman ilimi wajibi ne ga dukkan musumi."


Matsawar ka amsa kiran Manzon Allah (S) wajibinka ne ka nemi ilimin addini dana zaman takewa. Domin Allah baya karbar aiki sai mai tsarki.

Taya zaka maida ayyukanka su zam tsarkaka? Nemi ilimi, ta hanyar ilimi ne zaka tsarkake ayyukanka kazam cikin amincin Allah, da hanyar kaucewa aikata saba masa.

Allah kaine mai yassare wa bawa ilimi, ka wadata mu da ilimummukanka, ka saka in munyi ilimi muzam masu aiki da abinda muka sani alfarmar shugaban masu Ilimu habibinka Muhammad dan Abdallah (S).

Bιπ 卄α尺οπ 丂ιᎶαυ
08065008703

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post