Cewa Sayyid Ibrahim Yaqub El-zakzaky.H.
To in ka sami cewa zaka iya zuwa kai ka kashe mutum bakwai a kan kai ba ka ma sanshi ba, bakaji ma ta bakinsa kuma an taba yin hukunci a hukunta mutane a dunkule? kamar mu qaddara akwai wata qungiyar mutane sai aka sami wani mutum a cikinsu ya fadi wata magana to kowa ya fadi wannan maganar kenan (acikinsu?) ba shi wanda ya fadi maganar shi kwai za a dauko ?
Mu qaddara wani ya quqe yana wa'azi sai ya fadi wata kalma kuma kalmar nan ta zama muganyar magana kalma wadda a nazarin masu hankali da masu ilmi wannan maganar ta fidda shi addinin musulunci to kuma ta fidda duk wanda yake sauraron sa? Mu qaddara in kaji kalmar mummuna ko da a rediyo ne kai ma ka zama wannan? ai ka ga shine ya yi laifi shi zaku kamo shi kadai sannan shi ne za a yiwa hukunci a kotu ba kowa da kowa bane. ba a taba hukunta mutanen gari ko qabila ko al'umma ko yan wata qungiya ba wannan shar'a kenan.To ku ina kuka sami hujjar kuna iya zuwa ku kashe mutam?
Ina fadin wannan na wala'alla zakuyi hankali.Ba wai muna jin tsoran kar kuyi kisa bane muna so kuyi hankali ne kar kuje kuga abin da yake ba makawa ba ku kuma da maguda ba ku da matsera in kun gan shi shine sakamakon Allah gobe qoyama.
FREE ALLAMA SAYYID ZAKZAKY.H