Me Buhari yake Nufi da Shugaban Yan Shi'a a Nigeria??
-Hassan Muhammad Ghulam
Ma'asumah Nigerian news update
Wallahi mallamai da sarakuna kufito kuyi magana akan lamarin Sakin sheikh zakzaky kafin haqurin yan shi'a yaqare kunsan dai sunyi haquri iyakar haquri game darashin Adalcin da aka musu dangane da kama mallaminsu babisa qa'idaba tunbayan shekaru biyu da suka wuce akakamashi akan tare hanya sannan Kuma yanzu bugu da qari Court tabada umarnin asakeshi shida iyalinsa Amman Gwamnatin tasa taqi.
Inakira ga mallaman Addin muslunci kusani cewa lamarinnan baqaramin abu bane amma kunyi burus musamman ma mallamaina na Ahlissunnah da sauran dariqu bawai ana. maganar aqida bane walau Kai Dan izala ne, salafiyyane, shi'ane, tijjaniyyane, ko qadiriyya a'a ana maganar gaskiyane kawai, wallahi duk masifar datasami qasarnan kusani dasa hannuku idan har bakuyi abunda yadace akan wannan Bawon Allah ba.
Ina qara farkar da muku idan ba'a dakatar da wannan abunba haka an sake musu mallaminsu to Nigeria tana gab da fadawa masifar da ba'ay tsammaniba walau daga mutane walau Kuma daga ALLAH saboda nafadi wannanne bawai innuna cewa yan shi'a zasu maida martanin abinda Aka musubane a'a Bahaka nake nufiba.
Amman dai kobakomai kunsa waye Dan Adam?
ba yadda Za'ayi Azahar gida aka shemaka Yaya har uku da almajirai sama da mutun Dari bakwai Tareda wasu ba'adin daga cikin yan uwanka Kaima a harbeka kaida Matarka Kuma atafi daku atsare batare da wata tuhuma ba amman ace kayi haquri yazaka kwatanta abunnan azuciyar ka balle Kuma acema ba'a yima komaiba saboda kai kajawo akanka?
Kuduba wannan al'amarin fa ko kafiraine su ko wayan da Basu da Addini bazamuce hakaba balle musulmi in antabamu sai muce waida Dan shi'a gwara Christer (WA'IYYA ZUBILLAH ) To Abin tambaya anan awane fadin kenan, nason rai ko na Allah da manzon sa?
OK Ince ya ake zama musulmi a garinku?
In antabaye mu sai muce suna zagin sahabbai amman ba wannan batun bane agabana ba yanzu ba kuma ina karesu bane a'a ni kawai ayi 'adalci.
*INKAINE WANI MATAKI ZAKA DAUKA*
in kaine wane mataki zaka dauka yayin da kake da goyon Bayan milyoyin almajiranka wadda ko wuta kace su shiga zasu Shiga da gaggawa yayinda ka umurcesu?
Amman shk zakzaky yayi haquri a haka to mezaka fassara wannan haqurin nasa?
To yi tunani inshi yayi haquri to yaza kai da Mabiyansa Kuma wadanda akan idonsu akai komai ya zaka auna yadda sukeji zuwa yanzu?
kana nufin abinda aka musu zai tafi abanzane?
Wannan bahurumina bane amman zan iyacewa a'a.
To dan adam kenan yadda yakeji in an fusatashi yayin da akamai laifi to inaga Allah (SWA) Kuna nufin ahaka Allah zaibar abinnan yawuce kawai?
zan iyacewa a'a saboda dakansa yake cewa :-
ﺃﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻻﻳﻈﻠﻢ ﻣﺜﻘﺎﻝ ﺫﺭﺓ ﻭﺍﻥ ﺗﻚ ﺣﺴﻨﺔ ﻳﻀﺎﻋﻔﻬﺎ ﻭﻳﺆﺕ ﻣﻦ ﻟﺪﻧﻪ ﺃﺟﺮﺍ ﻋﻈﻴﻤﺎ < ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ / ٤٠
Sai a wani wajekuma yaqara cewa:-
ﻭﻣﻦ ﻳﻘﺘﻞ ﻣﺆﻣﻨﺎ ﻣﺘﻌﻤﺪﺍ ﻓﺠﺰﺍﺅﻩ ﺟﻬﻨﻢ ﺧﺎﻟﺪﺍ ﻓﻴﻬﺎ ﻭﻏﻀﺐ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﻟﻌﻨﻪ ﻭﺃﻋﺪ ﻟﻪ ﻋﺬﺍﺑﺎ ﻋﻈﻴﻤﺎ < ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ / ٩٣
Niba mallami bane basai na fassaraba saboda ina magana da mallamaine.
Ahakan manzon ALLAH (S) yakalli ka'aba yace yake kaba ranyen mumini guda daya awajen Allah (t) yafiki daraja da akashemin ran Dan adam guda daya bada haqqiba gwara arusamin sama daqasa walau Musulmi walau Christer.
haba yan uwa nidai mutane su shaida daga yau nabarranta da wannan zaluncin inkaga dama kakirani nima Dan shi'a.
Yanzu haka ance mallamin nasu yana buqatar likitoti qwararru domin duba lafiyarsa dangane da raunukan da akajimar tunbayan harbe harbenda akayimar abaya amman Likitoci sunyi umarnin da afitardashi waje saboda abin yafi qarfinsu anqi zuwa Yanzu to sai Ince to meyi Gwamnatin Nigeria take nufi ga Al ummar qasarta Bama ga Yan shi'aba?
Saboda tanashirin haddasa abinda shawo kansa zayyiwuya.
Kirana naqarshe dazanyi shine asaki mallamin yan shi'a wato sheikh zakzaky dashida Matarsa Tareda sauran almajiransa da ake tsaredasu saboda haryanzu Baku fadamana dalilin kamashi dakukayiba Tareda gamsar damu dalilin dayasa kuke riqedashi haryau dinnan dawannan nakecewa ALLAH yaganar damu gaskiya Kuma yabamu ikon binta yaganar damu bata Kuma yabamu ikon Kubucewa.
Tags:
Tunatarwa