Aqidar Muslimci ko dai Maguzanci ???


Yana daga cikin dalilan da yasa muke ankarar da 'yan'uwanmu masu da'awar cewa sune Ahlus-Sunnah kan cewa kada su halakar da kansu ta hanyar yarda da cewa akwai wani littafi tsarkakekke wanda babu kokwanto cikin abinda yazo cikinsa koma bayan Qur'ani. Duk wani littafin da ka sani matuqar ba Alqur'ani bane to babban kuskure ne marubucinsa yace wai duk abinda ke cikinsa ingantattu ne, ballantana makarantarsa su yarda da wannan fadin har ma a riqa ganin masu shakku kan hakan a matsayin wani abu dabam.

Duk wanda ya yarda da wannan aqidar da nake son kawowa to, lalle ya sami matsala cikin qwaqwalwarsa na cutar gubar gurbatacciyar karantarwa.

‘’ MAA QADRUL-LAHA HAQQA QADRIHI ‘’.

Bukhari ya ruwaito cewa, Abdullahi Bn Yusuf ya bamu labari, Malik ya bamu labari daga baban Zinaad, daga A'araaj, daga Abu Huraira cewa, lalle Manzon Allah (S.A.W.W)yace;

‘’ ALLAH NA YIN DARIYA ZUWA GA MUTANE BIYU DA 'DAYANSU YA KASHE 'DAYA KUMA DUK (biyun)SUKA TAFI ALJANAH. WANNAN YA YI YAQI NE A HANYAR ALLAH SAI AKA KASHE SHI, SA'AN NAN ALLAH YA KARBI TUBAR MAKASHIN (ya muslimta)KUMA YA YI SHAHADA (bayan kashe musulmin da yayi da kuma muslimtar tasa a fagen yaqin)‘’.

(Bukhari, hadisi na 2826).

         NAZARI
     ――――――

Allah (T)dai shine masanin komai da kuma qaddara shi, saboda haka ba zai taba yiwuwa ace abinda yasan da shi kuma ya qaddara shi sannan ace ya ba shi mamaki bayan aukuwar tasa har ya zamana yana yin dariya bisa aukuwar hakan ba.

Ballantana ma ya saba qa'ida ta tauhidi ace wai Allah na yin dariya ko zai yi ba, domin cikin wajibin da ke Kansa (T)ba.

A hankali da tunani na dan Adam ma duk abinda aka ce shi ya yi shi ba zai yi mamakinsa ta yadda har zai yi dariya kan hakan ba. To, ina kuma ga Allah wanda komai ke kasantuwa bisa ikonsa da qaddararsa?

A riqa yin tunani dai wajen qirqirar magana a jinginata ga Allah (T)ko kuma Manzonsa (S.A.W.W).

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

08137925034-08126385470

~ 27th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post