BABU MAI IYAGOGAYYA DA ITA A CIKIN SU
1- Ita ce Matar Annabi ta farko.
2- Ita kadaice Annabi ya Aure ta tana
Budurwa.
3- Itace Mahaifiyar 'Ya'yansa duka (In
banda Ibrahim a.s.).
4- Ita ce ta riga dukanin mata yin
Imani da Annabi (Sallallahu Alaihi
Wa'aalihi).
5- Annabi bai yi mata Kishiya ba
saboda matsayin ta a gurin Allah.
6- Ita ce Kakar Khalifofin Annabi (11)
na (12) kuma Sirikin tane.
7- Ita ce Kakar duk Sharifan duniya
gaba daya.
8- Ita ce Mahaifiyar Shugabar Matan
Duniya (Fatimatuzzahrah
Alaihassalam).
9- Tana daya daga cikin (4) na
Shugabannin Matan Duniya.
10- Ita Ce Ta ba da dukan dukiyar ta
wajan taimakon Addinin Allah.
11- 'Yar ta ce (Sayyida Zahrah)
Hurul'inun Mutane (Haura'ul
Insiyyah). Tafi kowacca mace Kyau.
12- Annabi yafi Son ta fiye da sauran
Matansa saboda Kyawawan Halayan
ta.
13- Bata taba busata Allah da
Manzansa ba koda sau daya.
14- Ayar Zargi ko Aibantawa bata taba
sauka a kanta ba.
15- Ita ce wacca Allah ya yi mata
Bushara da Aljannah tun tana Duniya.
16- Ita Ce Kakar Hasan da Husain
(Alaihihimassalam) Shuwagabannin
Samarin Aljannah.
17- Ita Ce Tafi Duk Sauran Matan
Annabi Kaunar Annabin.
18- Ita Ce Mai 'Ya (Fatimatuzzahrah
Alaihassalam) Da Babu Irin Ta A Duk
Fadin Duniya.
19- Ita Ce Tun A Jahiliyyah Kabilar Ta
Suke Kiranta Da Sunan "Addahirah"
Saboda Kamalarta.
20- Ita Ce Bayan Wafatinta Annabi
Yake Cewa Allah Bai Bashi Wata Mata
Irinta Ba Bare Wacca Tafi Ta.
Ya Allah ka kara tsira da aminci ga
Sayyida Khadija Alaihassalam ka kara
haske da yarda a Kabarinta da
Ruhinta ka kara Kusantar da ita zuwa
gare ka Ya mai jin kan masu jin kai.