Masu neman Duniya sun Jure azaba Da kuntatawa a Wanna Duniya bare Kuma masu neman lahira !??
___
A kasar nan anyi wasu jama'a masoya wani
shahararren dan siyasa a jihar kano wato malam Aminu kano wanda ya jagoranci jam'iyyar siyasa mai suna NEPU inda suka kalubalanci Gwamnatin su sardauna a kan zalumchin da take tafkawa a kan talakawan kasa da kama karya.
Babu irin bala'i da masifar da yan wannan
jam'iyya basu sha ba ta hanyar kisa kora da
kuma dauri amma basu juyawa jagoran su malam Aminu kano baya ba har ya bar wannan duniyar. Kai in nace har yanxu akwai sauran jama'arsa a wannan kasar banyi karya ba.
Malam Ibrahim yaqub El,zakzaky(h)shi kuwa
yana kiran mu ne zuwa ga neman tsira a gobe
kiyama da rayuwa mai yanci a nan duniya ta
hanyar bautawa Allah makadaici,kuma malam bai
boye manufar sa ba ta ganin Addinin Allah yayi
iko da wannan kasar wanda Allah ne ya shimfida
ta.Bin dokokin Allah sau da kafa ne zai kawo
karshen duk wani nau'in zalumchi da talauci da
yayi ma al'ummar kasar nan dafifi.
Malam din nan da harshen hausa yake magana
ba da yaren mala'iku ba balle ace ai ba a
fahimtar me yake cewa amma da yawan al'umma sun kawar da kan su daga barin jin gaskiya da riko da ita.
Ta hakane a kullum almajiransa ake kashe su,ana wawashe masu dukiya da kona masu gidaje da wajen kasuwancin su ta hanyar amfani da fatawowin malaman fada.
TO KUSANI YADDA SARDAUNA BAI IYA BUSHE
HASKEN MALAM AMINU KANO DA MASOYANSA
BA,TO HAKA WADAN NAN AZZALUMAN BA
ZASU IYA DUSHE HASKEN WANNAN BAWAN
ALLAH DIN BA.
LALLAI ZASU YI BAKIN KOKARIN SU AMMA FA
BA ZASU YI NASARA BA.DOMIN DUK ABIN DA
SUKA YI MA MALAM ZAKZAKY(H)KARA
DAUKAKA NE DA MATSAYI A WAJENSA DA
ALMAJIRANSA KUMA INSHA ALLAH DUK NAU'IN
CUTARWAR DA AKE MASA ZATA ZAMA TARIHI
KAMAR YADDA YAU GASHI CUTARWAR DA AKA
YI MA MALAM AMINU KANO DA MASOYAN SHI
TA ZAMA TARIHI.
YAN UWA MU KARA HIMMA NASARA NA KUSA
DA GAGGAWA KADA MU DAMU DA CUTAR
MASU CUTARWA A GARE MU.ALLAH SHINE
GATAN MU!
Tags:
Tunatarwa
Yane
ReplyDelete