ZAIYI MAKA WAHALAR GANE WANNE KAFI TSANANIN BUƘATUWA ZUWA GARESHI

ZAIYI MAKA WAHALAR GANE WANNE KAFI TSANANIN BUƘATUWA ZUWA GARESHI


Ma'asumah Nigeria News Update 
Tare Ishaq Muh'd Suleiman 

 Numfashi ko Addu'a 
Ɗan Adam Nada buƙatuwa zuwa ga Addu'a kamar yadda yake buƙatuwa zuwa ga numfashi Domin yadda yayi imani da cewa bazai rayu ba sai da numfashi
To haka kuma bazai kai ga gaci ba matuqar baya Addu'a, 
Kuskuren mu shine
Sau da yawa bama lazimtar Addu'a sai damuwa ta taso mana, 
Shiko yin addu'a yayin buƙata kamar fafar gora ne ranar tafiya, 
Bazai wadatar ba
Addu'a, ajiyarta akeyi a asusu kafin zuwan buƙata saboda haka ne da buƙatar tazo sai Addu'ar ta yanke maka buƙatar, Wannan yasa nassoshi da yawa suka bawa Addu'a siffofi kyawawa masu gaye da tasiri misali Addua3 takobin mumini
Addu'a bargon ibada
Wannan yasa Ahlilbait (AS) suka tsara mana tsarin Addu'a Kamar haka, 
Kafin Salloli
Cikin Salloli
Bayan Salloli
Na ko wacce rana
Daren Juma'a 
Ranar Juma'a 
Fararen Darare
Lokuta Zaɓaɓɓu
Da Makamantansu,

Ƴan Uwa Kada mu Manta Da Yiwa Jagora (H) Addu'a, Allah ya bashi lafiya Alfarmar A'immatul Huda

Ma'asumah Nigeria News Update 
Ishaq Muh'd Suleiman 
Wakilin mu Na Sokoto 
08132933333 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post