Daukar Darasin Dake Cikin (Like) yafi Fa'ida.
Ma'asumah Nigeria News Updates
Wato da yawa idan mutum yayi rubutu (post) sannan ya sami yawan masu goyon baya (like) ya kan ji dadi sosai, kuma hakan na qara masa qwarin gwiwa wajen qara yin wani rubutun.
Da ace mutum zai riqa rubutu (post) akai-akai, san nan kuma ya kasance ba ya samun masu nuna goyon bayansu (like) ko kuma rashin yin sharhi (comment), to, da ba lalle ne aga mutum na yawan rubutu ba.
A gaskiyar magana wasu ba suna goyon bayan (like) rubutu ne don fa'idarsa ba, a'a, don ra'ayi ni wanda ba ya amfanar da komai/kowa face wanda yayi rubutun.
Akwai rubutun (post) da wasu ke yi mai ma'ana da fa'ida, amma sai kaga ba a kulawa dasu don a qarfafi mai wannan aiki wajen qoqarin cigaba fa'idantar da al'umma.
Ba qyashi ko hassada nake yi muku ba mata, amma saboda gaskiya yasa nake qalubalantar abokanku maza.
Da yawa wasu mata kanyi rubutu (post), wanda in ka nazarce su sai kaga babu wata fa'ida ko kadan, amma sai kaga yawan goyon baya (like) daga mazaje.
Na'am, akwai kalma da mutum zai iya rubutawa mai ma'ana wanda zai fa'idantar da jama'a fiye da yadda wani zai yi dogon rubutu.
Saboda haka nake gargadin 'yan'uwa mata da su kasance masu amfani da wannan damar da Allah ya ba su na farin jini wajen isar da saqon harka fiye da saqon nishadi.
Isar da saqon harka wanda zai fa'idantar da al'umma ya fi amfani da ki yi rubutu wanda zai jawo miki yawan magoya baya (like), amma in an nazarce shi ba shi da amfani a harkance ki a addinan ce.
Mai karatu kafin muci gaba Danna photon Nan na kasa domin yin Like din Page dinmu dake Facebook.
Wadanda suke mu'amala ko nace masu yin rubutu a (pages) za su fi saurin fahintata, domin mutum zai yi rubutu kuma ya sami maziyarta aqalla 300, amma bai sami goyon baya (like) fiye da 20 ba.
A taqaicen taqaitawa, ina qoqarin fahintar da masu rubutu ne kan cewa su kasance masu yin rubutun da zai riqa fa'idantar da al'umma ko da kuwa ba za a goyi bayanka ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
081263
October 13