Yadda da Saurayi na Shi yajaman Dana Sani !! labari Na ya zamo darasi gareki Kawata.


Cewar Baby S. Kamal.

_Daga Shafin Ma'asumah Nigeria News update

Namiji!!! kalmar da zan fara furtawa daga bakina
kenan,lallai yan hausa sunyi gaskiya da sukace da
nasani keyace, ko shakka babu haka abin ya ke,
Duk da cewar nasan mekaratu zai sha mamaki ta
yadda ya ji na fara da sunan kalmar NAMIJI.

Haka abin ya ke Hakika akan samu maza na Allah wanda
har kullum fatana ko yaushe Allah yabaki miji nagari
mesanki sabo da Allah, wanda wannan addu'ace da
ya kamata Kowacce mace ta lizimtawa kanta domin
yin hakan ya nada gayar muhimmanci. Baya ga haka
kasance kamila me mu'amala da kamilin mutum.
A kwana a tashi yan hausa na cewa wata rana jariri
angone. Na kasan ce na taso a gidan mutumci,
gidan manya gidan da kowa ke girmamawa, tare da
cewar mahaifina ba wani me kudi bane face allah ya
yimasa rufin asirir daidai bakin gwargwado, ya
bamu tarbiya dai bakin ko karinsa musamman
karma mahaifiyar mu ta ji labari, Babu wani abu da
bai dauke manaba haka rayiwar mu take gudana
gwanin ban sha'awa mahaifin mu ya kasance
mutum ne mai taimakawa ga wadanda basu da shi,
haka kuma mahaifiyar mu baiwar Allah ce wacce
batasan rowaba sam-sam wadan nan abubuwan
yasan mahaifinmu ya zamo abin kwatance a
unguwar mu, mun kasance mu 6 dane a gidan mu,
tare da cewar mahaifiyata bata da wata kishiya. Na
kasan ce ni ce babbar ya a gidan mu, wanda a
lokacin ina da kimanin shekaru 17 a duniya Allah ya
min kira wanda kusan tun kafin, nakai shekara 17
ake nuna a na sona, hakika Allah ya yimin farin jinin
gaske wanda wasu naganin kamar ko iyaye nane
suka ne mamin wanda sam ba haka bane, face
Kawai daga Allah ne.

Akwana a tashi a rayiwata bani da wani buri face
naga na yi karatun addini me zirfi da na boko, a
wasu lokutan nakan ce da abban mu ni dai da
nagama (secondary school) burina na cigaba da
karatu wanda bakomai na ke san na karanta ba face
LAWYER. Ya dauki tsawan lokaci ya na nunamin
baby ya kamata kisan wani abu, ba na hanaki
karatu bane, burina ki yi aure in yaso sai ki cigaba
da karatun ki a gidan mijin ki.
Na kan ce da shi abba ba nace a'a ba amman
sakamakon ba ko wanne namiji ne zai a minta da
matarsa ta cigaba da karatun boko ba abba, domin
a gaskiya ina kishin kanmu mu mata abba, domin
ko menene mu ne abaya musamman a wannan
kasa, ya ce dani haka ne baby ni kaina ina kishi
naga mace ta nasan ta yi karatu Na addinin ta da na
zamanin amman ya kamata ki san cewa lokacin ya
mace ba kamar na da na miji ba, Fatana ki ta
addua Allah ya baki miji nagari me burin yaga kin
cigaba da karatu. domin aure bazai hanaki karatuba
maman ku kin sami labari tana gidan mijinta, ta
hada digreen ta na farko, ke dai ki cigaba da
addua'a Allah ya baki miji na gari. sakamakon
kunya bana iya cewa komai. Hakika abban mu
mutum ne da ya kan tattauna da mu domin jin
matsalolin mu abin mu gwanin bansha'awa.
Akwan a tashi, na yi samari da ban daban wanda ni
kai na bansan adadinsu ba. Sai dai kash!!! ni duk
basu kwantamin araiba, badan wai rashin Wani
abuba face, kawai jinina bai hadu da suba. Ana
haka muna gab da ga fita daga [secondary school]
katsaham sai Allah ya hadani da wani saurayi me
suna Abba.
Abba saurayi ne wanda shekarunsa basu gaza 25-27
Abba matashi ne, Fari kuma shi bai cika tsayiba
kuma ba gajerene ba, haka kuma Allah ya yi masa
kira wanda duk ya mace zataso tasami irin sa,
gashi da kirar jarimai me fadin girji dai dai misali
Abba dan kasuwa ne wanda shi ne babban yaro a
shagon uban gidan sa, wanda ya na samun kudi dai
dai bakin gwargwado. Katsaham Bayan mun taso
daga makaranta, Na sauka daga abin hawa, sai na
ji ana bina a mashin kirar lifan launin sa baki, bisa
ga dukkan alamu bai jima da siya ba.
Ya na sanye da Farar shadda, ga hula zanna bukar,
wanda bazan iya misalta launinta yadda ya kamata,
gashi sanye da agogo launin (golding color) ya na
sanye da wani bakin takalmi dan uban su. ban
ankaraba sai naji karar mashi abayana bisa ga
dukkan Alamu ni ake bi tun daga bakin titi har na
kusan isowa layin gidan mu, haka ya kara azama
cikin sauri ya sha gabana sannan ya yimin sallama,
DUBA GA YADDA BABU DADI MUTUM YA YIMA
SALLAMA KA KI AMSA MASA, SAI NA AMSA, NA
CIGABA DA TAFIYA TA, IDAN NA YI NAN SAI YA YI
NAN, CEWA YAKE DA NI DAN ALLAH KI SAURARENI
KI DAURE KI BANI MINTI BIYU, DUK DA CEWA
NASAN DAGA MAKARANTA KI KA TASO KUMA
NASAN BADAI DAI BANE NA TARE KI A HANYA
AMMAN YA ZAMO DOLANE GARENI WANDA WLH
BAZAN IYA HAKURIBA.
Na dube shi cikin daure fuska tare da yan kwana
fiskata na ce ok... Ina jinka me ke tafe da kai? ya
ce dani cikin sigar murmushi, kayataccen albishir.
Na ce da shi mlm sauri na ke ina da bunyi, cikin
sauri ya ce nasani ranki ya dade. Da farko sunan
Abba Haka cikin sauri ya zai ya nemin cikekken
sunan sa na gaskiya, da inda ya ke, ya ce dani idan
badamu ya na son ya san inda na ke, karshe
sakamakon wulakanci babu kau haka na kwatan
tamasa karshe sai da ya ga na shiga gida sannan
ya tafi ko da ya ke, ya yi yi na bashi lambar wayata
na ce da shi, bani da waya yanzu. Haka karshe ya
hakura ya tafi abin sa.

Bayan kwana biyu da haduwata da Abba ranar
alkhaimis katsaham sai akace ana sallama da baby
maman mu ta ce wa dan aiken ya je yace wanene?
nan take dan aiken ya ce wai Abba ne, ni kuma a
lokacin ina tsaka da karatu. Maman mu tace baby
ki tashi ki je ana sallama da ke, na ce mama
amman su mutane basu da tsari ko wanne lokaci
kawai sai suzoma mutum? maman mu ta ce ki yi
hakuri tashi ki je domin wulakanta mutun babu
dadi. Haka na tashi batare da ina soba na dauki
hijibana
MU HADU AKASHI NA BIYU DAN JIN YA ZATA
KAYA BAYAN TAFITA KUMA BAYAN NAN ME
KUMA YA BIYO BAYA?
*NI NE NAKU HARKULLUM HABIB RABIU
NASRALLAH.*

Email:habibrabiu81@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post