by Aminu Ibrahim
Wani abin al-ajabi ya faru a garin gano bayan an gano wani mutum mai suna Aminu Baita da aka ce ya nutse a rafi ya mutu tun a shekarar 1990. Wani na kusa da iyalansa, Yakubu Musa ya ce baita wanda kwararren mai aikin jinya ne a asibiti ya samu matsalar kwakwalwa kafin bacewarsa daga gidansa da ke garin Danbatta, kilomita 70 daga birnin Kano. Mista Musa ya ce, "Aminu ya mutu ya dawo 'yan makonni da suka wuce. Ana iya cewa dan uwa na ya taso daga mattace." "Kafin bacewarsa, Aminu yana aiki da ma'aikatar lafiya na jihar Kano a 1980s. Ya yi aure kwatsam sai ya fara nuna wasu hallaye da ba a saba gani ba. "Daga bisani ya rasa aikinsa kuma aurensa ya mutu duk da kokarin da aka yi na neman masa lafiya. Wani mutum ya mutu ya dawo bayan shekara 30 a Kano
"Daga baya sai aka kai Aminu gidan masu fama da matsalar kwakwalwa a Danbatta. "An fada mana cewa Aminu ya sulale daga gidan kuma ya daja tsalle ya fada rafi kuma ba a gano gawarsa ba.
A matsayin mu na musulmi sai muka rungumi kaddara muka yi addu'ar Allah ya jikansa. "Kwatsam kuma sai lamari ya canja. Daya daga cikin yayi na, Nasidi Musa ya tafi karamar hukumar Toro a jihar Bauchi don neman wani surukinsa da ya bace da aka ce an gano shi a can.
"Da ya tafi bai gano sirikinsa ba amma sai ya gano 'dan uwansa da 'ya mutu, Aminu. "Nasidi ya dako shi sun dawo tare da labari mai ban mamaki. A yanzu da na ke magana, Aminu yana asibitin kwakwalwa na Kazaure bayan an dawo da shi daga Toro. "Abin mamaki shine bai manta sunan iyayensa ba da na kawunsa da har da mahaifi na. A lokacin da suke hanyar dawowa yana ta tambayar su.
"Mutanen garin da muka dako shi inda ya kwashe shekaru 30 yana zama ba suyi muryar rabuwa da shi ba. Labarin da muka ji shine ya zauna cikinsu kamar nan ne garinsu na tsawon lokacin da muke tunanin ya 'mutu.
Madogara
Madogara