Shin, A wane Hali Mlm Zakzaky Ke Ciki Ne ??

_____________________
Ma'asumah Nigeria News updates

Wannan tambaya ita ce wacce jama'a da dama ke yi, kuma cikin su har da 'yan adawa, magoya baya da kuma mabiyansa (H). Kowa na son sanin halin da yake ciki gwargwadon abinda ke cikin zukatan su.
Wasu na son sani ne don suyi murna in yana cikin mummunan yanayi, wasu kuma don su jajanta, yayin da wasu kuma ke son sani don su qara qaimi na fafutukar da suke yi don ganin ya kubuta (free).
Tun bayan dawowar Sayyid (H) daga India zuwa wannan lokaci, daga cikin irina babu wanda ya isa yayi bayanin takamammen halin da yake ciki zuwa yanzu.

A baya kafin tafiyar tasa za ka riqa cin karo da rubuce-rubuce a kafofi da dama wadanda ke bayyana halin da yake ciki, walau bayanin na qarya ne ko gaskiya. Amma a wannan lokaci babu wani bayani wanda wani zai dorar a gaba, na dadi ne ko na muni.

Na'am, abinda dai nake da yaqini shine, ba za a rasa wasu masu qoqarin ganin cewa an sake fita da shi don nema masa lafiya ba, domin da dadewa na taba ji/gani a Alwilaya TV anyi hira da wani Barrister da yake bayanin hanyoyin da suke bi.
Tun bayan wannan shiri ban qara ganin makamancinsa ba. Hatta a social media bana ganin wani rubutu dake nuna halin da wannan salihin bawa ke ciki. Sanin halin da yake ciki kuwa na da matuqar muhimmanci gare mu.
TO, MENENE MAFITA?
_____________________
Cigaba kan abinda aka saba a baya irin su:-
Muzaharori,
Rubuce-rubuce,
Addu'o'i da kuma,
Bayyana zaluncin da akayi masa da almajiransa ta haryar wa'azozinmu na da matuqar muhimmanci.
Sannan kuma mu jure mu dake kan koyarwar da yayi mana ba dare da qosawa ko gaggawa ba, domin sau da yawa gaggawa ba ya haifar da da mai ido.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~ 15th October, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post