SHAIKH YAKUBU YAHAYA DA SULHU DA GWAMNATI !!!


✍️
— Saifullahi M Kabir

Kanun Jaridu daban-daban a ranar Asabar 19 ga October 2019 sun bayyana dangane da wani tattaunawa da aka yi da Wakilin yan uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a garin Katsina, Shaikh Yakubu Yahya, inda mafi yawa suka nuna cewa Malamin ya bayyana bukatarsu na tattaunawa da gwamnati. Shin hakan ya faru?

Na saurari hirar da aka yi da manema labaru a ranar Assabar, a Markaz din Katsina, wanda yake da tsawon Mintoci 32 tare da Shaikh Yakubu Yahya Katsina. Kuma a cikin hirar Malamin ya yi bayani a kan abubuwa daban-daban. Daga bisani akai masa tambayoyi ya ba da amsa.

Malam Yakubu Yahya ya fara bayani ne da magana a kan asalin Tattakin Arba'in din Imam Husaini (AS) da kasancewarsa Sunnah a addinin Musulunci, tunda Sahabi Jabir Bin Abdullahi ne ya fara yi daga Madina zuwa Karbala, da kuma Iyalan Manzon Allah (S) a shekara ta 61 bayan Hijira. Don haka Malam Yakubu yace: "addini muke yi, ba yana nufin cewa in gwamnati bata so kawai sai mu dena ba." Yace muna aiwatar da abin da muka fahimta addini ne, ba rigima muke ba. "Ba mu ke fada da gwamnati ba, ita ke fada da mu.... Ko jiya a Abuja sun yi kame-kame, sun yi harbi."

Yace ba yadda za a yi mun san muna da addini mu bar addini mu koma ma abin da gwamnati ke bukata. "Gwamnatin Kasar nan su kawo aya daga Attaura, ko Injila ko Zabura ko Alkur'ani cewa yadda suke gudanar da mulki haka Allah Ya ce a yi. Muna jiran amsa daga gwamnati da ma'abotanta. In suka kawo mana za mu ga ashe mune muke a kan bata, sai mu bari, ko muce muma ga namu a raba da shi. Amma idan babu, to ba yadda za a yi mu da muke da Hujja saukakka mu bar abin da muke yi muyi wani abu da shi bai da Hujja bai ma da dalili."

A nan ne kuma ya jaddada cewa "Muna so mu tabbatar da cewa shi kashe mutane saboda addini yana bunkasa addinin ne. Ba a taba dankwafe Akida da karfi ba, kowace iri kuwa."

Ya cigaba da cewa: "Ba a dankwafe Akida da karfi, ana zama ne a tattauna, a ga ina za a tsaya, ya za a yi? Haka kasashen masu hankali suke yi. Amma nan (Nijeriya) ban san ko wace irin kasa bace. Bata bin dokokin Allah, wanda ta tsara ma kanta ma bata bi. Ban san wace irin kasa muke zaune ba. Allah Ya sauwaƙe."

Bayan kammala wannan jawabin na Shaikh, Wakilin Radiyo Faransa,
ya tambaya a kan wane hali Shaikh Zakzaky ke ciki tun da ya dawo India? Sannan an yi batun zama a tattauna ake yi. Yace shin kuna shirye ku tattauna da gwamnati?

Malam Yakubu Yahya ya ba da amsa da cewa akan halin da Malam Zakzaky ke ciki tun bayan dawowarsa daga India, inda a ciki yake cewa: "Ciwon da ake ma magani ne ake masa zaton warkewa, a iyakan saninmu, tunda ba a kai Malam wani asibiti ba da ya dawo, kuma ba a masa magani ba, ciwonsa na nan yadda yake ciwonsa."

Sannan ya juya batun tambaya a kan tattaunawa, yace: "Dangane da abin da ya shafi ko sasantawa da Gwamnati ko wani abu, ba mu taba rufe kofar mu ba, kullum kofarmu a bude take duk wanda ke son a tattauna da shi shirye muke mu tattauna, in yana bukata. In gwamnati na son a tattauna da ita, wannan Harkar bata taba rufe kofar ta ba, kofa bude take a zauna a tattauna, a ga ina ne aka samu rashin fahimta. Mu dai mun fahimci gwamnati, mun san ta, yanzu ma kaji na yi bayani akan manufofinta. Ita ce bata san mu ba. Ya kamata mu zauna ta fahimcemu, mu kuma ina muka sa gaba, me muke yi?"

Duk da wannan amsar, sai dan Wakilin Daily Trust ya Kuma tambaya a kan tattaunawa. Nan ma Malam Yakubu ya maimaita masa cewa: *"Abin da nake cewa shine, kofarmu a bude take don tattaunawa da gwamnati a kowane lokaci, ba tare da wani sharadi ba kuma. Kofarmu bude take su zo a tattauna, saboda mu mun fahimci wace ce gwamnati, mun fahimci mece ce gwamnati, amma ita gwamnati ta ki ta fahimce mu, su suka jahilce mu. Sune basu yarda su gane me muke yi ba, amma mu mun san su, mun san ko su su waye. Kuma kofarmu a bude take, wanda duk ya miko hannun aminci, za mu mika masa hannun aminci. Wanda ke son tattaunawa za mu tattauna da shi, ya fahimce mu ya san me muka sa gaba. In ya so sai a samu matsaya, sai ya zama al'umma kowa ya zauna lafiya. Abin da muke bukata kenan, ba mu son abin da zai dami Kasar nan. Bamu da wata kasa sai wannan, kuma ba za a yi amfani da mu wajen rusa Kasar ba. Mu yan kishin kasa ne na hakika."

Ina tambaya: shin akwai abin rudewa a cikin wannan bayanin? Mene ne illarsa? Shin in abin gwamnati ta nemi a tattauna ne Harka za ta ki ne? A baya da gwamnati ta nemi a tattauna a kan wasu abubuwan an tattauna ko ba a tattauna ba? Waki'ar Quds na bayan nan 2014, bayan haka ba su kafa wata kwamitin jeka na yi ka ba? Sun nemi wakilcin Harka ko ba su nema ba? Malam (H) bai tura wasu yan uwa su Wakilce shi a zaman da aka yi da Sojoji ba, duk da ya san shiririta ne kawai abin?

Yanzu a cikin Waki'ar Zariya din nan da ake ciki, ba a tattaunawa ta wasu janibobi da Wakilan da Malam ya ayyana? Ba a filin Wa'azi Farfesa Dahiru Yahya yake bayyana yadda suke tattaunawa da gwamnati ba? Gaban kansa yake yi a tattaunawa din? Ko laifin cewa kofar mu a bude take da duk mai bukatar tattaunawa, gwamnati ce ko wasunta, saboda ya fito daga Malam Yakubu Yahya ne kawai? Yaushe wasu mutane za su yi hankali ne? Yaushe gubar gaba da cutar hassada zai fita a zukatansu ne?

Ko 'yan Jaridu ne suka ruda ku? Kun mance yadda muke fama da Jaridu a kan juya maganganu ne? A dirar mana su ce an yi arangama? Kun manta su ke cewa mun addabi mutane, mun tare hanya? Mun yi kaza da kaza? Shin Labaransu ba tare da kun binciki gaskiyar al'amari ba ya kai mutum wai shi Buraza ne yai ta kumfar baki ga Malamin Harka kuma? Har Malam (H) bai kubuta daga sharrin Jaridu na canza magana ko ma'anar magana ba. Mu lura mana yan uwa?

Yan Jaridu sun yi wa Malam Yakubu tambayoyi da dama, ya basu amsa. Ciki har da Wakilin Aminiya da yace, Duk lokacin da za a yi arangama, yawanci in ana Tattaki ne. Shin baku da wata hanya na yin abubuwa dole sai an yi wannan Tattakin?

Shaikh Shaikh Yakubu Yahya yace masa: "Bari na maka gyara. Ba arangama muke ba, gwamnati ke kawo mana hari. Don arangama shine makiyi ya fitar da makami, nima na fitar da nawa, a kwama, shine arangama. 'Clash' kenan. Don haka ba arangama muke ba, ita ke kai mana hari."

Yace masa: "Cewa bamu da wata hanya da za mu bayyana al'amarinmu sai ta wannan Tattaki din. Eh, bamu da ita. Saboda shi addininmu haka ya tsara mana. In an yarda muna da addini to a bar mu mu yi. In ba a yarda ba muna da addini ba, sai ai doka a hana mu, ko a yi doka a ce addinin da mu muke tafiya a kansa gwamnati ta haramta, ga addinin da ta halasta, shi take so a yi."

Suka ci gaba da tambaya a kan ya dangantaka yake da makwafta? Meye hangen Malam a kan kai samame da gwamnati ke wa wasu makarantun allo? Dalilin da yasa wasu yankuna ke Tattaki, amma Katsina ke taron Arba'in? Yadda yan uwa suke kallon abin da gwamnati ta bayyana kwanan baya na cewa ta haramta Harkar Musulunci ta mai da ta yar ta'adda, da kuma hasashe kan adadin mabiya Harkar Musulunci a Najeriya a yanzu. Duk Malam Yakubu ya basu amsa.

Don haka ya dace mutane su saurari audio din nan ne mai tsawon minti 32. Na tabbata za su fahimci abin da aka ce yadda ya kamata. In ma raddin zai yi sai ya ji daɗin yi, maimakon kawai ya duba Kanun Jaridu irin su Aminiya da BBC ko DW yai ta haushi da sunan yana wa Malam Yakubu martani.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post