SABUWAR RANAR DA ZA A FAFATA WASAN EL'CLASICO

Wasan Clasico ya koma ranar 18 ga watan Disamba

Hukumar kwallon kafar Spain ta sanya ranar 18 ga watan Disamba a matsayin ranar da wasan Clasico tsakanin Real Madrid da Barcelona zai gudana bayan matakin sauya masa lokaci daga Asabar din nan mai zuwa sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Catalonia.

Wasan wanda tun da farko aka tsara zai gudana a filin wasa na Camp Nou na Barcelona Laliga ta nemi mayar da shi filin wasa na Real Madrid don gudanar da shi a ranar da aka tsara amma kuma Barcelona ta ki amincewa da matakin.

Yanzu haka dai hukumar Laliga ta bayyana cewa za ta shigar da kara kan matakin na hukumar kwallon kafar Spain don kuwa ita ta mika bukatar mayar da wasan ne ko dai ranar 4 ko kuma 7 ga watan Disamba maimakon 18 da hukumar ta zartas.

Dalilin dayasa aka Dage wasan Elclasico.

An tsara za'ayi wasanne a 26 ga watan nubamba, a babban filin wasa na Kamfunu mallakin Kungiyar kwallan kafa ta Barcelona.
   Andage wasan ne sakamakon zanga-zangar da akeyi a Birnin kataluniya dake Barcelona na neman ballewa daga yankin Spain dominsu kafa kasarsu.
    Wannan daliline yasa aka Dage wasan harsai 18 ga watan Dusamba.

Post a Comment

Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post