Kamar Yadda muka nado Daga Jaridar primeums Time Hausa, Rahotanni daga jaridu daban daban, sun bayyana cewa Nanono ya furta kalamai cewa wasu ‘yan Najeriya da ke kukan yunwa, abin dariya ne .
Ministan na harkokin noma ya ce tabbas babu wata yunwa a Najeriya.
Ministan na harkokin noma ya ce tabbas babu wata yunwa a Najeriya.
Da ya ke magana a wurin taron Ranar Abinci ta Duniya a Abuja, Nanono ya kara da cewa, “Ina jin mu na noma abincin da za mu iya ciyar da kan mu. Ina ganin ni dai babu wata yunwa a Najeriya. Idan mutane su na magana ko korafin cewa ana fama da yunwa a kasar nan, ni dariya ma su ke ba ni.”
Ana bikin murnar zagayowar Ranar Abinci ta Duniya a kowace shekara, wajen 16 Ga Oktoba, domin tunawa da ranar da aka kafa Kungiyar Abinci da Ayukan Gona ta Majalisar Dinkin Duniya, cikin 1945.
Kungiyoyi da dama masu ruwa da tsaki wajen batutuwan samar da wadatar abinci ciki har a Shirin Samar da Abinci na Duniya da Gidauniyar Duniya ta Inganta Harkokin Noma duk su na gudanar da bukukuwan zagayowar ranar.
A cewar Nanono, abinci arha ya ke yi a Najeriya, idan aka kwatanta da wasu kasashe. “A kasar nan da dan kudin ka kalilan sai ka sayi abinci ka ci ka koshi.” Inji shi.
Ya ce gwamnatin tarayya ta yi tunanin rufe kan iyakokin ta ne saboda kasashe makwauta sun maida Najeriya wajen jibge kayayyaki da shinkafar da lokaci ko wa’adin cin ya wuce.
Haka nan kuma kafofin yada labarai da dama sun ruwaito Nanono ya na cewa saboda tsananin arhar abinci, a Kano za ka iya cin abinci da naira 30, kuma hark a ci ka koshi.
Tags:
Labaran Duniya