Karanta Cikakkiyar Firar da mukayi da Wani Buraza da ya koka game da Auren Sistoci!!
Ganin yadda ake qyamatar shi'ah da 'ya'yanta sakamakon batanci da maqiya ke yi da sunan wa'azi ko jahilci yasa har mu kayi hira kan haka da wani dan'uwa.
Nine na fara ce masa malam, kai me kake gani ne game da auren 'yan'uwa mata (sisters), domin akwai abin tunani ganin yadda kullum qarin arziqinsu ake samu, ga shi kuma burazu raguwa suke yi ta hanyar shahada?
Naga wasun mu ba sa damuwa da neman su sai dai 'ya'yan amawa, alhali kuskure ne mai girma. Dalili kuwa shine, idan muka ce amawa za mu aura ya makomar 'ya'yanmu da 'yan'uwan mu sistoci zai kasance?
Sai yake ce min;
" To, ni dai a gaskiya bana buqatar na tsaya da sister da sunan nema, sai dai muyi ma'amala ta 'yan'uwantaka a harka, kuma har shawarwari zan iya ba su.
Batun nema kuwa, ko da za a zarge ni sai dai ayi, amma ba zan zubar da mutuncina wajen nuna kai gare su ba. Zai fi min mutumci na nemi wadanda ake kira amawa."
Da na tambaye shi dalilin wannan ra'ayi nasa sai yace;
" Kai za kaga kamar taimakon juna ne in ka nemi 'ya'uwa, amma su a tunaninsu shine kamar qasqanci ne gare su in sun auri mutumin da yake da mata. Ni kuma ina sai ina gani kamar laifin iyayensu mata ne, domin da ace suna dora su kan daidai da har da wannan matsala za su riqa bijiro musu don su kiyaye.
Su kuma 'ya'yan amawa da iyayensu har neman ka suke yi. Yau idan kace ko ka nuna kana son yarinya cikin amawa sai kaga har mutunta ka ake yi daga mahaifanta.
Wani lokaci ma su iyayen yaran ne ke zawarcinka suna cewa ga 'yammata nan kuna gani amma ba mai nema cikin ku?
To, yanzu dan Allah da inda za kaje a mutunta ka da kuma inda za ka je ana walaqanta ka ko kuma gani kamar an fi ka, alhali a tunanin ka ba abinda za su nuna maka ta bangaren karatu ko dadewa a harka, ina ya kamata ka je?
Nace maganar sa gaskiya ce, amma dai kuskure ne ace mu bar sistoci mun koma ga amawa, domin barin nasu zai yi sanadin komawarsu hannun amawa, don ba zai....
Zamuci gaba....
Daga wakilinmu
Ado Isa guda
Na'am wannan ra'ayin na wannan bawan Allah ne shi kadai. Muna bukatar a kawo mana wani dalili wanda ya zama general wato wanda ya ratsa ta ko ina. Ba lallai bane ya zama cewa duk sistoci suna da wannan halin ba, domin ban taba fuskantar wannan halin tare da su ba.Shi dai abinda ya fuskanta kenan.
ReplyDeleteWannan gsky ne ra'ayin wannan Dan uwa su awurin su abin tozarci ne sukula Dan uwa kuma duk halinsu daya ne naga da dama daya cikinsu anan potiskum jahar yobe don haka wannan ba korafin da su sisters zasu fitar bane mune ya kamata muyi musu wannann tambyr insha Allah.
ReplyDeleteMUSA HARUNA IMAM POTISKUM.
Malan jafar
ReplyDelete