Magani Muka dura masa, Inji Ummul Muminina Aisha, (Shahadar Manzon Allah)!!!


SHAHADAR MANZON ALLAH (S.A.W.W), 28TH SAFAR, 10 (A.H)  !!!

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MAGANI MUKA 'DURA MASA IN JI UMMUL-MUMININA A'ISHA

Ita mutuwa al'ada ce wacce dukkan wani mai rai sai ya dandana ta, Mala'ika ne, Aljan ne ko kuma bil-Adama, har ma dabbobi da tsirrai da kuma qwari (insects).

Hanyar mutuwar ce ta kasancShahadare daban-dabam, wani ya kan mutu irin mutuwa ta dabi'a, wani kuma ya mutu ta hanyar wani, wato kamar ta hanyar hatsari (accident) ko ba shi guba (poisoning) ko kuma a dora makami a kansa (assassination or homicide). Wani lokaci kuma mutum yakan kashe kansa da kansa (suicide) saboda wani dalili nasa.

To, mutuwar Manzon Allah (S.A.W.W) ta kasance ne ta hanyar dura masa magani da aka yi da wata manufa wanda hakan yayi sanadin shahadar sa.

Hakan kuwa bai zama abin mamaki ko baqin ciki ba, domin hakan da aka yi masa ne ta qara masa matsayi na daukaka, wato mutuwar shahada.

Bukhari ya riwaito cikin Sahihin sa yace, Aliyu ya bamu labari, Yahya ya bamu labari yace  A'isha ta ce;

" Magani muka dura masa (da qarfin tsiya) a halin jinyar sa. Yana ta nuni gare mu cewa;

" KA DA FA KU 'DURA MIN MAGANI (saboda ya san manufar mu."

Mu kuma (saboda manufar da ke cikin zuciyar mu ) sai muka ce, a'a, irin qin shan maganin nan ne na marar sa lafiya.

To, yayin da ya farfado (don ya tabbatar mana da munin aikin mu kafin yayi shahada) sai yace;

" ASHE BAN HANE KU CEWA KADA KU 'DURA MIN MAGANI BA "! 

Sai muka ce ai muna ce irin qin shan maganin nan ne na marar sa lafiya. Sai yace;

" BABU WANDA YA RAGE CIKIN GIDAN FACE YA YI WANNAN 'DURE (gare ni), INA KALLO (ban fita daga cikin hayyaci na ba), SAI DAI KAWAI ABBAS (daga cikin ku), DON SHI BAI YI TARAYYA DA KU (cikin wannan mugun aiki) BA."

 (Bukhari, hadisi me lamba 4458).

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      08126385470

~ 27th October, 2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post