KWAIKWAYON KWALLIYA DAGA BIRNI ZUWA KAUYE, AN SA'BA LAMBA!





(c) Hafiz Koza.

09094608450 / 07060438556

To shin me ya sa aka sa6a lambar ne? Wato abinda nake hasashe ya jaza hakan abubuwa ne guda uku:
-Rashin Sani.
-Rashin Bincike. Sai kuma
-Raina kauyawa da mazauna birane suka yi.
.
A inda rashin sanin yake shi ne, masu alakanta kowace irin kwalliya da zaman kauye, ba su mu'amalanci zaman kauyen ba kwata-kwata. Duk da haka kuma sai masu son kwaikwayon suka ki yin bincike dangane da sahihancin yadda suke kwatanta kwalliyar da ake yi a kauye. Ita wannan kalar kwalliyar (Wacce ake ya6a mai a fuska, a bursuna hoda, a jajja6a jambaki, a d'id'd'iga bak'in tukunya a kumatu da goshi; a sa kaya daban-daban, a daura zane ba daidai ba, a daura kallabi a yamutse...) tabbas ana yin irin ta a kauye, amma fa ba koyaushe 'yan matan kauyen ke yin ta ba. Suna yin irin wannan kwalliya ne a rana ta musamman, wato washegarin kai amarya gidanta, lokacin da abokan ango ke zuwa shan fura, to sai su yi irin waccan kwalliyar, idan abokan angon sun zo a yi hira, su sha fura sannan su biya, su tafi, daga nan sai 'yan matan su wanke wannan kwalliya. Ko a da din ma irin wannan kwalliya yan mata sun ba ta suna da, 'Kwalliyar Hauka', har kawo yanzu kuwa haka ake kiran ta. Makasudin yin kwalliyar kuwa ta zama kamar wata alama (Symbol) da ke nuna cewa a garin ko kauyen an yi sabuwar amarya, ke nan ko da wani bako ya zo gittawa zai shaida hakan, sannan kuma yin kwalliyar na zama kamar wani abun nishadi da ake yi matsayin cikamakin shagulgulan bikin aure. Inda raina kauyawa da mutanen birni suka yi ya zo kuwa, kamar yadda na ambata a baya, bai wuce yanzu a shagulgulan biki da ake a birane, har da wata tabbata da ake yi, wai 'Kauyawa Day!'. Sai mutum ya ga fird'a-fird'an yan mata sun jajja6a hoda da jambaki da jagira da bak'in tukunya a fuskarsu, a yi wani fitinannen daurin kallabi, a sa zane daban riga daban, a na juyawa da k'yar saboda manyanta da jikin girma; amma fa duk a haka wai yan matan kauye ne ake kwaikwaya. Abinda ba su sani ba shi ne, su da ke irin wannan kwaikwayo fa idan sun zo kauye, to iyayen wasu ne! A kauye yarinya na fara kirgar dangi manema za su fito, a ciki za a samar mata miji managarci a ba da ta gidan aure, ba kamar birane ba da kasuwar yan mata ke nauyi. Ai duk wani shagali da ake, ana fitsara a yayin bukukuwa a birane, to mazauna karkara na daukar abin kamar #'Audition' ne ko kuma #'Auction_Sale'. Wato yan matan na samun damar nuna #'treasure' dinsu ga mahalarta, su tallata kansu ko an samu mai tayawa. Da wasu 'Kauyawa Day'; da wasu 'Fulani Day'; duk k'arya ce! Da za a daina su, sai an fi zama lafiya.
.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post