Ko 'Yan uwana Sisters Mun Fahimci Hakan?


A duk lokacin da kika fito sanye da Hijab da Cikakkiyar Shigar da Addini yazo mana dashi zaki ga babu yadda za'ayi wani Saurayi ya tare ki a hanya da maganar Soyayya, koda Saurayi ya ganki yana sonki indai Saurayin kirki ne bazai taba yi miki magana a hanya ba zai biyoki gida kafin ya nemi soyayyarki sai ya sanar da Mahaifinki yana Neman iznin zuwa Ku fahimci juna, domin kuwa da mutuncinki ya ganki kuma yasan cewa daga gidan mutunci kika fito 

"Sabanin Macen da fito da shigar da bata dace da Musulma ba, zakiga Gayu suna binta a titi da sunan suna sonta a kalla kafin taje wurin da zataje tayi samari uku a hanya, kuma idan kika duba zakiga duk cikinsu babu mutumin kirki 

Wasu suna ganin kiyi kwalliya ki fita samari su rinka tareki a hanya shine Wayewa har ana yiwa wadda batayin hakan kallon bata waye ba, zakiji Kawayenki da suke irin wannan shigar suna cewa kinsan Samarin yanzu sunfi son suga budurwa da gyale tayi kwalliya tana rausaya a titi 
Nasan dai Wadannan Samarin basu suka halicceki ba Allah (T) ne ya halicceki to 'Yar uwata Umarnin waye zaki bi ki samu dacewa? 
Shine Umarnin Allah, kenan kinga Wadancan Samarin da kikeyin Abu dan ki birgesu ba koyarwar Addini bane 

Duk da wasu 'Yan Matan suna ganin sai da dressing din zamani Samari zasu ganki suce suna sonki a titi 
Kwarai hakane domin kuwa idan mace tayi shigar Kamala Tana kara kwarjini ne a Idanun Mutane babu Namijin da zai iya tunkararta a titi da wani magana saboda kwarjininta Kuma duk inda ta shiga mutane suna girmamata da mutunta ta domin itama ta mutunta kanta 

 Sabanin ke da kikayi Shigar zamani kika sanya gyale ko Half Sunnah kowanne irin mutum zai iya tareki kuma koda ba mutumin kirki bane 

Misalin Macen da tasa Hijab da wadda bata sa ba kamar Alawa ce acikin Leda da wadda ba'a cikin Leda take ba 
 duk Wanda yasan abinda yakeyi ta ledar zai siya ya bar wadda take ba'a Leda ba
Sai mun zama nagari zamu samu 'Ya'yaye nagari.

Nasiha

-Daga Wakiliyar mu Fatima Xahrah Shi'ite

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post