Kashi na 2, Babban kuskuren Dana tafka a gidan Miji na...!!


_Daga shafin ma'asumiyya news updates_

A wancan karan mun tsaya a gun da mubarak ya
dawo gida a gajiye da kyar ya samo abin da za'aci
a gidan, amman da da wowar sa, ko hutawa bai
gama yi ba, tare da cewar ko abinci bai gama ciba
amman khalisat, ta fara kawo masa bukatunta,
kamar su kayan kwalliya da ankwan bikin kawarta
d.s wanda karshe sakamakon bacin rai, mubarak ya
tashi daga wurin khalisat ya nufi daki bacci, to zan
dora daga nan_*.


Da isar mubaraka dakin bacci bai wani bata
lokaciba ya zauna a gefan gado, ya yasa hannunsa,
bib-biyu ya dafe kansa, ka na ya sun kuyar dak kansakasa, ya na bub-buga tafukan kafarsa akan
(capet). Duk da irin wannan hali da mubarak ya
shiga, ban yi la'akari da wannan ba, haka na tashin nabishi har ya zuwa dakin bacci, na tarar da shi, a
yanayin da na same shi, cikin ban tausayi amman ni
ko a raina, bana tausayamasa, wanda nasan da
cewar duk macan arziki bazata so, a irin wannan
yana yi ta kawo mijin ta bukatun taba, kamata ya yi,
a ko da yaushe ta kasance ta na kwantar masa da
hankali, amman ni ko ajikina, domin ni burina guda
daya ne Mubarak ya sauwakemin, domin a gaskiyab bazan iya rayiwa a cikin bakin talauciba, batare dala'akarin nima iyayena talakawa bane, amman
sakamakon san duniya da nake da shi, baisa na yi la'akari da wannan ba, kawai ya sauwake min, kod daya ne, ina takama da masoya domin ina ganin dazarar na gama idda insha'allah sai dai kawai adauramin aure.

Baya ga haka ban yi la'akari da
jarrabawar da Allah ya yiwa mubarak ba, domin daya ya na da kudi amman sakamakon, jarrabawar da
Allah ya yi masa ya shiga halin da ya shiga amman
ni ko ajikina, bandamuba.
Haka na same shi ya yi tagumi ya sun kuyar da
kansa kasa, ya dafe kan sa, da hannu bib-biyu, a
lokaci guda kuma ya na bubbuga tafin kafarsa, haka
na same shi, na tsaya kansa ka na, na kama
kuguna da hannu biyu, da ya ke a lokacin ina sanye
da doguwar riga, launin ruwan toka, na dan yafa dan
kwalin ta, akan kai na, su kuwa yayan mu dama
basa gidan suna gidan mahaifiyar sa. haka na dubi
mubarak na ce da shi cikin fushi, na ce ya za ayi
ina maka magana ka taho ka barni, kasan da cewa
ankwan nan idan banyi shiba da matsala, wlh bazai
yiwu naje biki na fita daban ba, bashi za ka ci me
zaka yi wannan bai da meni ba, ni dai kawai ka
siyomin.
kafin nagama rufe bakina, bansan lokacin da
mubarak ya mike tsaye ba, ya dallamin mari, tare
da dunguremin kai, ka na ya ce da ni cikin fushi,
ANKONE BAZANYI BA, ANKI AYI DUK ABIN DA ZAK KIYI KIYI. Haka ya sa kafarsa ya fita ya barni a
dakin, hannuna na kan kuncina hawaye na
gangarowa daga idanuna, haka ya barni ina shish-
shidar kuka.

Duk da wannan abu da ya faru baisa na karaya ba, bayanwasu lokuta, bayan na ci kuka na, na godewa
Allah, kimanin karfe shadaya 11:32pm haka
zuciyata ta yanke hukuncin na dauki biro da takarda
na kaiwa Mubarak ya sauwake min, wanda ni
daman abin da nake buri ke nan. Wanda a iya
tsawan rayiwar mu tsakanina da mubarak, baitaba,
dakamin tsawaba, ko zagi ko wani abu me kama
da haka ballanta na duka, wanda tabbas nasan da
cewa lallai nakai mabarak makura.
Haka na dauki biro da takarda na bude kofar dakin
da nake ciki, cikin fushi, budewata ke da wuya sai
na hangi mubarak, a falo ya na zaune akan doguwar
kujera, ya yi shiru abin duniya ya yi masa yawa
domin hattama a gidansa da yakamat ni na kwantar
masa da hankali, amman sakamakon san duniya ya
sa na watsar da wannan haka na nunufi, wurinsa na
tsaya, sannan na jefamasa biro da takarda akan
kafafunsa na ce da shi, cikin Fushi.
MUBARAK IDAN KA HAIFU CIKIN HAJIA DA ALHAJI
KA SAUWAKEMIN NAGAJI DA ZAMA DA KAI, BA NA
SANKA BANA KAUNAR KA, KA SAUWAKEMIN.
Dajin haka mubarak dan danan hawaye suka fara
gangarowa daga idanun sa, dan danan idanun sa,
suka kada sukayi jawur, cikin dan kan kanin lokaci,
wanda a iya rayiwata da shi bantaba ganin bacin
raisa ba irin wannan mai mutukar ban tsoro, ga duk
wanda ya kalli mubarak kai kace wanda zai ta da
iska.
Mubarak ya dubeni, cikin matsananci fushi, ya ce da
ni, khalisat NI KI KE GAYAWA IRIN WADANDAN
MAGANGANUN KO? NI KI KE GAYAWA HAKA KO?
NAGODE ALLAH YA HADA KOWA DA RABANSA A
KURKUSA, KA NA YA CI GABA DA CEWA, TABBAS
MUTUM BAYA GANE MASOYINSA NA HAKIKA, SAI
LOKACIN DA YA SHIGA CIKIN WANI HALI ANAN
ZAKA GANE MASOYINKA NA GASKIYA.

Haka ya tashi tsaye ya nufi dakinsa wanda a iya
zatona bantaba zatan mubarak baxai sauwakemin a
wannan daran ba, amman haka yasa hankalinsa ya
kuma sa tunani, bai sauwakemin ba.

Duk da haka
ban sadudaba. Domin duk idona ya rufe.
Da wayewar gari, da misalin karfe 7:30sf mubarak
ya fice wanda na yi mamakin fitarsa da wuri haka.
Wanda bashi ya dawoba sai dare.
Haka muka cigaba da rayiwa, ina kuntatamasa iyak kuntatawa duk wata kafa da zan bashi, domin ya
ga farincikina, na tosheta, wanda shima mubarak na
mijine, shima sai ya fita daga harkata gabadaya tun
bayan da na bashi takarda, ya sauwakemin karshe
dai abu yaki ci ya ki cinyewa, harsai da takai,
mahaifiyata ta na xuwa, ta yimin nasiha, ta yimin
fada amman duk abanza, tun mahaifina baisan abin
da ke faruwa, har sai da takai mahaifiyata tasanar
da shi.
Mahaifina bai bata lokaci, ya kira mubarak a waya
domin ya zo ya na bukatar ganin sa. haka dai ya je
bansan me suka tattauna ba, domin ni duk da haka
burina guda daya ne mubarak ya sauwakemin. gaba
daya idona ya rufa.
Wata rana da misalin karfe 8:04 pm mubarak ya
dawo gida, da dawowar sa gida, sai ya bukaci da
na bashi abincin dare, budar bakina na ce da shi
bandafa ba, domin yau na yi baki, baya ga haka na
gaji, bana jin dadi sosai, haka na tafi abuna na
barshi a falo, shidai mubar ya kasa cewa komai,
sabo da tsananin bacin rai. Can ba'a jimaba sosai,
bayan ya fita ya samo abin da xaici da daddare, ya
shigo cikin daki na, ya yi sallama, amman ban
amsa masamasaba, da shigowar sa, ina kan gado a
kwance, duk ilahirin jikina suna kallan sama, da
shigowar sa, na juyamasa baya ka na na yi tsaki,
mubarkar ya dauke kansa daga gareni, ya xauna a
gefan gadon da na ke kwance, fuskarsa na kallan
kudu.

YA CE DANI KHALISAT, GOBE IDAN ALLAH YA
KAIMU DA SAFE KIJE GIDA ZANZO.
Mubarak ya sa kansa ya fita daga dakin, a dai dai
wannan lokacin, na ji badadi amman ta wata fuskar
na ji dadi domin ina ganin da Alama karshe
xamanmu yaxo karshe domin ina gani, da xarar mun
rabu zan sami mijin da ya fishi.

Da wayewar gari, mubarka ya zo yasaman ya
mikamin naira 1000 ya ce dani gashi wannan ki hau
mota. Haka ya ajiyemin ya fita abin sa ya koma
dakinsa ya yi zaman sa.
Bayan wasu lokuta nagama shirye-shirye na, na tafi
gidan mahaifana, na bar mubakar a gidansa...


ABIWO NI A KASHI NA UKU DON JIN YA ZATA
KAYA, TSAKANINTA DA IYAYANTA, ZA SU KOMAR
DA ITA GIDAN MIJIN KO KUWA ZATA ZAUNA A
GIDAN IYAYANTA?
By Habib Rabiu Nasrallah
Email:habibrabiu81@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post