*KANO KAFIN ZUWAN MALAM MUHAMMAD MAHMUD TURI*
Mutum ba zai iya gane matsayin ko wanene Malam Turi ba ko kuma wane irin aiki yayi a kano da Haraka baki daya ba sai yasan Halin da Kano take kafin zuwan Malam Turi. Yan'uwa Mabiya Malam Zakzaky (H) na Kano sun kasance cikin rudani, rashin hadin kai,rashin girmama juna, bangaranci da rashin Nizami kafin zuwan Malam Turi. Kasantuwwar kowace irin fitina ta haraka zakaga Kodai an kirkireta a Kano ko kuma nan aka yayeta. Misali:- Fitina zuhudu, Yan Malam bai shi'a, Yan Malam bai sunnah,Tawiyiyya, Takaladiyya, Shi'a- sunnah da sauransu etc. Kuma kowacce akwai burbushinta a cikin da'irar kano.Kuma kowa yana da jama'arsa a harka,Ga kuma wakilan jahilliya a Sassake cikin kowane bangare suna rura wutar fitina.Don haka koma na yan'uwa hatta Pre-Huduba biyu ko ukku akeyi.A Kano ne farkon tunzura farar hula suyima Malam (H) bore da niyyar kasheshi a BUK da kuma Technical ace rikicin cikin gidane sanadin mutuwarsa.Ganin haka yasa Jahilliya batasa karfi a Kano ba a lokacin waqi'ar Abacha ba,saboda komai take so akwai masu yi mata a cikin Yan'uwa. Amma duk sauran Da'irorin Kasar ta tarwatsasu ta takura ta turasu kurkukun ta hana ayi komai banda kano. Su an barsu amma a boye jahilliya ke juyata yadda suke so. Yan'uwa sunzama crowd kawai wani lokaci t hada yan'uwa fada da mutanen gari,sufaye, ko izala,wani lokaci kuma ta hadasu fada yasu yasu suyi doke doke da zage zage. Misali:- wata ranar jama'a naje kano lokacin Abacha, a massalacin Fagge sai na samu ranar yan'uwa anyi sulhu tsakaninsu a ranar an maido pre-kuhdba daya. Malam Adamu Garko Wakilin yan'uwa na Garko a lokacin shine ke jawabi (Tsohon Dan'uwa ne ada) yana tsakar jawabi akan hadin kai da illar rarraba,Yan'uwa sun barsu ana Jindadi wahada ta samu.sai naga kuma naji wani mutum mai Bakar hula daga gabas yayi tsalle da hargowa ya na zagin Abubakar da Umar sai daga amma wasu mutum biyu da jajayen huluna suka dauko itace sukace su sai dai a mutu. Suna raye ba za a zagi Sayyadi Abubakar da Sayyadi Umaru ba, har suna zagin Jafar Saddiq basu yarda a zagi sahabbaiba. A takaice wuri ya yamutse yan'uwa da itatuwa suna dukkan junansu. Nazo tasha zan shiga mota sai naga mutum Hudun da sukafi zakewa a waccan rigimar masu baka da jar hula gasu a mota daya. Bayan sati daya aka kamani aka kaini Headquarter ta farin kaya ta katsina sai ga daya daga cikinsu shinema case nawa yake hanunsa.
Wannan kadan kenen ga halin da Malam Turi ya samu Kano amma cikin cikin ikon Allah ya hada kan Yan'uwa da mutanen gari, malaman sufaye dana izala, masarauta, Yan kasuwa,Yan boko da sauransu. Ba shakka Malam Turi ya maidoma haraka kimarta da mutuncinta a kano, ya daukaka matsayin harka a ilmance da tarbiyance hatta tattalin arziki. Ta kai yan'uwa kamar sune jama'ah mafi tasiri a kano. Misali:- Lokacin bude massalacin Alh.Bashir Tofa ya gina, kano ta hadu da manyan malamai, na birni ga sarakan kano, manyan yan kasuwa da yan bokon kano sun hadu Sheik Turin na bayani sunyi tsit. Sarki Sanusi Yayi Quri yana kallo da sauraren Sheikh daga ni kasan yaga ilimi da shiriya.
*KADAN DAGA HANYOYIN DA MALAM TURI YABI YAYI NASARA*
1)Wata rana Mahaifiyar maigidana ta rassu naje ta'aziyya. Ina tare da maigidana sai babban shehin wata Dariqa a kano yazo bayan ya gama ta'aziyya ga jama'a sai suka kebe da maigida dai dai inda nake, mu ukkune sai naji Shehi yace "kuyi hakuri badanku naki fitowa ba, wadannan mutanen masu kwakwar tsiya sau tara suna zuwa bana fitowa amma sunki fasawa, so suke mu fito suyi photo su aika iran a basu kudi " Shehi dai yayi ta batanci ga haraka sosai. Akan haka raina ya baci, naje nasamu Malam Turi nayi masa bayani har nace tur da Shehin nan baida wuta ko aljanna, kaskancine a liqe masa yana wulakantamu bisa shawara kawai a rabu dashi. Sai kawai Malam Turi ya kira wani yace aje a bincika masa ko shehinan nanan zasu zo ziyara zasu cika na goma, kuma zasu kara komawa ko bai fito ba.
Anan take kuma ya bani hakuri ya nunamani ita nasara daga Allah ne namu kawai aiki.A takaice bayan sati biyu sai naga almizan naga hoton Malam Turi da wannan Shehin watau anyi ziyarar, ta kuma bada ma'ana har takai Wannan zawiyya in zasuyi programme dinsu har jiran Malam Turi suke.
2)An taba bani gabbatar da Malam Turi a taron Ahlul Duthur da akayi a kano a wajen gabatarwa na fadi wasu falaloli da ya kebenta dasu kamar nace"hannun damansu Malam(H) masanin boko masanin musulunci kuma yafi kowa fahimta da biyayya zuwa gasu Malam (H)" sai ya tsaidani haka. Bayan antashi ya kirani yace intuna kano nike inbar irin wanan. Sai nace ai gaskiyace na fada, sai yace wani bayaso shikuma su Malam sun turosu hadin Kaine ba wargazawaba, tsamo yan'uwa daga fitunu ba rudasuba don haka abinda haka abinda na fada gaskiyace amma zata iyasa wani ya rasa imani koma yabar haraka, saboda furucina, yin haka mun taimaki su Malam(H).ko mun cuta masu? Nabada hakuri.
3)Akwai wani mutum cikin yan'uwa na kano wanda yana kiyayya da batanci da karya, kazafi ga Sheikh Turi. Wata rana anzo zama sai wanan mutum yazo makare ga kuma wurin ya matse sai mutane sukaqi kulashi, Malam Turi yace a matsa masa sanan Malam ya dauko dardumar da yake zaune ya shinfidama maizaginsa har yace sadaukinsane kuma suna alfahari dashi da kokarinsa. A takaice daga ranar Dan'uwa ya cigaba da zuwa markaz ada kuwa ya kaurace.
Yan'uwa musamman masu tafiyarda al'ammurransu akwai darussa sosai daga rayuwar Sheikh Turi ga mai neman shiriya.
*Adamu Lamama*

Tags:
Jagoran Gaskiya