Kabar murna don Karen ka yakama Zaki..!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED 

Mulki da makami ya zama shine babban abinda fajirai ke tinqaho da shi a wannan duniya. Wanda ya mallake su sai ya mance da cewa wanda ya ba shi wadannan abubuwa biyu ya fi shi qarfi da iko kan kamai.

Kafin mutum ya sami mulki ba za ka taba jin sunansa a matsayin wani jarumi ba, amma da zarar ya samu sai ya ji cewa yanzu zai iya kashe kowa ya murtsike su don babu mai iko a kansa.
Wannan dalili yasa wadannan fajirai ke ganin babu wani mai qarfin su.
Allah (T) ya bamu labarin Adawa wadanda ya hore musu qarfi har suke iya fafake dutse suyi ginin dakunan kwanan su, har suke tinqaho da wannan qarfi nasu suna cewa!

" TO, AMMA ADAWA SAI SUKA YI GIRMAN KAI A CIKIN QASA BA DA WANI HAQQI BA, SUKA CE; " WANENE MAFI TSANANIN QARFI DAGA GARE MU?" ASHE KUMA BA SU GANI BA CEWA ALLAH WANDA YA HALICCE SU SHINE MAFI QARFI DAGA GARE SU? SUN DAI KASANCE MASU YIN MUSU GAME DA AYOYIN MU.
SAI MUKA AIKA A KANSU DA ISKA MAI TSANANIN SAUTI DA SANYI, A CIKIN WASU KWANUKA (rana ku) NA SHU'UMCI, DOMIN MU 'DANDANA MUSU AZABAR WULAQANCI A CIKIN RAYUWAR DUNIYA. KUMA LALLE AZABAR LAHIRA ITA CE MAFI WULAQANTARWA, KUMA SU BA ZA A TAIMAKE SU (daga wannan azabar) BA ."
(Fussilat, aya ta 15-16)
Ku ma nan ba da jimawa ba za ku zama tarihi.
WANNAN DAI TUNATARWA CE.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470

~ 22nd October, 2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post