Gareku Mata dama mazan, Shiga domin Karantawa, ayi shere domin Wasu su Amfana.
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
Kalmar jahilci abu ne mai girman gaske, kuma mai fadin ma'ana.
Masana na cewa babu wani dan Adam wanda za ace masa jahili, domin Allah (T) bai taba yin dan Adam wanda ya barshi sakakai ba tare da ya ilimantar dashi wani abu ba. Yayin da kake tunqaho da ilimi kuma kake ganin wani a matsayin jahili, to, sai kaga ya aikata wani abu na ban al'ajabi wanda duk tarin karatunka ba za ka iya yinsa ba.
Wannan dalili yasa babu wani mutumin da za ka ambace shi da kalmar jahilci face ya ji wani abu ya tokare shi a qahon zuciyarsa, idan kuma kana musantawa hakan, to, ka kira wani da wannan kalma.
A mahanga ta shari'a, ko da ace mutum ya zama professor ne a karatun zamani (boko) amma babu ilimin addini tare da shi, to, shi jahili ne. Shi ma wanda yayi karatun addini amma ba ya aiki da shi, shi ma ya shiga cikin jerin jahilai wadanda auren su ya zama illa.
Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa,
" BA WANI ABU BANE ILMI FACE AIKI DA SHI."
Kenan duk wanda ba ya aiki da abinda ya karanta ya zama jahili.
Aure da ya kasance ibada kuma wata hanya ta neman samun yardar Allah wacce cikinsa kuma ake fadawa cikin fushin sa ya zama dalili wanda yasa muka ga ya kamata mu ambaci wasu kalmomi kan wannan, domin ankarar da mata masu neman mazajen aure.
Wannan doguwar shimfida ta haskaka mana sanin wanene jahili. Sai ku kasance tare damu cikin rubutun mu dake tafe don sanin illolin aurensa.
Muhadu Kashi na biyu
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
~28th September, 2019.