Idan kabi Azzalumin Shugaba Kuma batacce, Za kuyi Jayayya Da Shi a ranar Alkiyama!


Babu riba cikin biyayya ga azzalumin shugaba, domin ba zai iya amfanar da kansa bama ballantana ya amfanar da kai a lahira. Saboda haka, yin bara'a gare su a duniya shine 'yancin ku, kuma tsirar ku a lahira.

GA DAI YADDA ZA TA KASANCE TSAKANIN KU RANAR SAKAMAKO
Allah (T) na cewa;
" KUMA SUKA BAYYANA GA ALLAH GABA 'DAYA (mabiya da wadanda aka bi), SAI MA SU RAUNI (mabiya) SU CEWA WADANDA SUKA KANGARE (shugabannin zalunci), " LALLE NE MU MUN KASANCE MA SU BI NE A GARE KU (a duniya), TO, SHIN,KU MASU KARE MU NE DAGA WANI ANU NA AZABAR ALLAH (tunda kune shugabannin mu)? (Azzaluman shugabanni) SUKA CE, " DA ALLAH YA SHIRYAR DAMU DA MUMA MUN SHIRYAR DA KU, (saboda haka) DAIDAI NE A KANMU (mu da ku) MUYI RAKI (wajen kasa jure wannan azaba) KO KUMA MUYI HAQURI (na azabar da muka shiga) BA MU SA WATA MAFITA (wajen tsira) ."
MAGANAR SHAIDAN A KANSU
" KUMA YAYIN DA AKA QARE AL'AMARI (hukunci) SAI SHAIDAN YACE; " LALLE NE ALLAH YAYI MUKU WA'ADI, WA'ADIN GASKIYA (cewa ku bi shi ta hanyar bin jagoran gaskiya), KUMA (ni shadan) NAYI MUKU NAWA WA'ADIN (na qarya) SA'AN NAN NA SABA MUKU. KUMA NI BA NI DA WANI DALILI (iko) A KAN KU (na tilasta ku cewa kubi azzalumai), SAI DAI KAWAI NA KIRA KU NE (kan haka kamar dai yadda jagoran gaskiya ya kira ku), SAI KUKA AMSA MIN (nawa kiran ku ka qi amsa kiran gaskiya). SABODA HAKA KADA KU ZARGE NI (don ba tilasta ku nayi ba), KU ZARGI KANKU (don ku kuka ga damar bin umarnin nawa). NI BAN ZAMA MAI AMFANAR DAKU BA (a yau), KU MA BA KU ZAMA MA SU AMFANAR DANI BA. NI NA BARRANTA DA ABINDA KUKA YI TARAYYARSA DA NI KAFIN (wannan rana). LALLE AZZALUMAI SUNA DA AZABA MAI RADADI."

(Suratul-Ibrahim, aya ta 21-22)

Ma'asumah Nigeria News updates

Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~22nd October, 2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post