Hankali Shi ne Babbar Wadata,



BABU TALAUCIN DA YA FI JAHILCI

Hausawa na yin wata karin magana da cewa; " SHARI'A SABANIN HANKALI ".
Lalle ko da ace a mahanga ta nazariyya karin maganar ba ta dace ba, to, bisa abinda nake son kawowa a qasa za muce tabbas karin maganar ta yi daidai anan.
Kun san a tunanin da mafi yawan mutune ke yi shine, tarin dukiya ita aka fi sani da wadata, amma anan ba haka abin yake ba.
Imam Ali (A.S) yana fadawa dansa Imam Hassan (A.S) cewa;
" YAA 'DANA! BABU WADATA DA TA FI HANKALI, KUMA BABU TALAUCIN DA YA FI JAHILCI, KUMA BABU ABIN TSORO DA YA FI GIRMAN KAI, SANNAN BABU RAYUWA MAI DADI DA TA FI KYAWAWAN 'DABI'U."
(Biharul-Anwaar, J:78, Sh:111)
NAZARI
_________
(1)- Idan muka kalli maganar farko cikin wannan hadisi za mu iya cewa, hankali ya fi dukiya, domin da hankali ake iya sarrafa dukiya. Ko da ace mutum ya tara dukiya amma ba shi da hankali to, ba zai iya sarrafa dukiyar yadda za ta amfanar da shi a duniya da lahira ba.
(2)- Babu talakan da ya fi jahili cikin al'umma. Duk mutumin da ya kasance jahili ne musamman ta bangaren addini wanda ta hanyar sa ake sanin Allah da yadda za a bauta masa, to, lalle yayi babbar hasara.
(3)- Girman kai shine mafi girma kuma abin tsoro tare da mutum, domin shine yayi sanadin halakar Shadan, kuma shine ke hana miyagun shugabanni da malamai karbar gaskiya.
(4)- Duk wanda ya dace da kyawawan dabi'u, haqiqa ya more jin dadin duniyarsa da lahira, domin ita ce babbar siffi daga cikin siffofin Annabawa (A.S), kuma ita ce ke yiwa mutum jagoranci zuwa Aljannah.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~ 21st October, 2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post