GWAMNATIN BUHARI YAKAMATA KICIKA ALKAWALIN KARIN ALBASHI DA KIKAYIWA MA'AIKATA.



Ana zaton wuta a makera amma sai gata a masaka, babu Wanda yayi zaton cewa wannan gwamnati ta Baba buhari zata zo da kwangaba kwanbaya a maganar Karin albashi, kasantuwar ma'aikatan gwamnati sunyiwa gwamnati halacci tun gabanin zaben 2015 har ya zuwa yanzu da ake wannan magana. Dayawansu sun kasa sun tsare wajan ganin tabbatuwar gwamnatin APC.

Sanin kowa ne cewa rayuwar ma'aikacin kasar nan tana fuskantar garari musamman kana nan ma'aikata da basu da hanyar satar kudin al'umma ko kuma hanyar cuwa cuwa, domin da yawa daga ma'aikatan kasar nan leburori MASU aikin karfi sun fisu kwanciyar hankali, kasantuwar yadda bashi ya dabaibaye ma'aikata, saboda karancin albashin da suke amsa daga hannun gwamnati, ga kuma kayan rayuwar yau da kullum sun ta'azzara fiye da yawan albashin da suke amsa. Kusan albashin yana tafiya ne a kan abinci kawai, babu maganar magani, makaranta, sutura, biki, suna, alkhairi, da sauransu. A haka ake rayuwa kusan ta YAUMU KUTUN!

Sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasa da kuma ka'idojin Karin albashin  ma'aikata yasa wannan gwamnati yin alkawalin Karin albashi mafi kankanta na naira dubu talatin, domin ganin an dan saukakawa ma'aikata kuncin da suke ciki na yau da kullum. Tabbas labarin Karin nan ya farantawa mutane rai, har mu da bamu taba daukar albashin ko sisin kwabo ba, munji dadi kwarai da gaske.

Bincike ya nuna cewa najeriya tana daya daga cikin kasashen dake biyan albashi mafi karanci Wanda baya Isar ma'aikaci yin rayuwarsa ta yau da kullum, amma duk da haka sai gaya wannan gwamnati da ma'aikata suka wahala wajan kafuwarta tana ta wasa da hankulan jama'a wajan wannan Karin kudi har abin ya kusa fita daga ran al'umma ana nema a zare jin dadin karin tun kafin Karin.

A magana ta gaskiya bai kamata ace an tsaya anata jeka ka dawoba, domin yanzu da wani tsarine gwamnati zata dauka don kanta da tuni abin ya fara aiki kamar yadda mukagani wajan Karin kudin man fetur, Karin kudin NEPA, Ga kuma Karin haraji shima zai fara aiki, kalli yadda aka rufe boda nan take, to mizai sa a ki biyan Karin albashi, alhali ga yan siyasa nan suna kwasar kudin banza da sunan alawuns alawuns, gwamnoni sunyi nade naden banza marar amfani, ga sanatoci da yan' majalissa suna karbar kudaden banza kuma ba tsiyar da suke aikatawa, idan har da gaske suke akan Kishin kasa da son al'umma to su rage kudadensu na bukata da wandakar da sukeyi, domin biyan mafi karancin albashin naira dubu talatin.  Matukar bazasuyi haka ba to karya suke akan cewa suna son talakka, saidai kawai ace sunaci da gumin talakka, ko kuma gumin kana nan ma'aikata.

Idan banda kin Allah da son zuciya ace albashin sanata duk wata dubu Dari shidda, shi kadai, ana kuma bashi kusan miliyan goma sha uku duk wata da sunan biyan ma'aikatansa da kudin hayar gida da sauran karyace karyace banza, haka idan ka tafi majalissar taryya Dana jahohi suma suna kwasar kudin banza, amma ma'aikaci maiyin wahala iya rayuwarsa a tsaya ana wasa da hankalinsa, akan Karin albashin da bai taka kara ya karya ba. kuma a haka akeso wai mutane suyi gaskiya, kai! Da sake.

Bai kamata ba a maida wannan Abu ya zama kamar wasan yara yau kusan wata bakwai ana Abu daya kamar cin kwan makauniya, ina kira da wannan gwamnati ta hamzarta magance wannan matsala kafin ranar litinin tunda yan kwadago sunce zasu shiga mummunan yajin aiki daga ranar laraba, idan kuwa har da gaske gwamnati tana tausayin talakkawa to kada ta bari a kai ga shiga yajin aiki, don yin hakan zai kara fito da wasu illolin gwamnati ne tare da nuna gazawarta. Tunda yajin aikin zai kassara tattalin arzikin kasa ne Wanda dama fama ake dashi ya tashi daga sumar da yayi amma har yanzu ruwa ake yayyafa masa, yaki tashi.

Ina kuma kira ga jam'iyyar APC tayi hattara domin a cikinta akwai yiwuwar yan ta wargaje sun zama akuya da fatar kura duk wani Abu da zaizo sai sunyi kokarin lalatashi don kada ayi nasara daga karshe idan ta bare can zasu koma inda sukewa aiki. TO BAHAUSHE DAI YACE KO BA MAGANA A ZURA IDO TA ISHI MAI HANKALI.

✍️ Musa Ibrahim Daura

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post