M.N.U 030
MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE
Duba da tabarbarewar tarbiyar zaman takewar aure musamman ma mu Hausa Fulani, zan so nadan yi mana bulala da tunasar damu wani hadisin manzon Allah (s) Wanda yake cewa: acikin khafi an ruwaito cewa imam Ali (a.s) yace: shida sayyida Zahara (s.a) sun ziyarci manzo Allah (s) yana kuka ta hanyar zubda hawaye bayan sun tambayeshi dalili sai yace: ya Ali a daren jiya na fita f
naga wasu mata daga al'ummah ta Wanda ake masu azabobi masu radadi da tsananin gaske sai naji tausayin su na fara kuka. Yaci gaba da cewa naga wata mace an sarkafe ta da nonon ta.sai mace ta biyu wadda take cin naman jikin ta kuma wuta na fita daga karkashin ta mace ta uku an sarkafeta da harshen ta kuma ana bata tafasasshen ruwan zafi daga makoshin ta ta hudu kuma an tankwashe ta an daure hannuwan ta da kafafun ta macizai da kunamu duk sun bai-baye mata jikinta. Ta biyar bebiya ce kuma makauniya an rufeta a kejin wuta kwakwalwar ta na fita daga ramin gashin ta, jikin ta na yankewa guntu guntu don kuturta.
Wata kuma an sarkafe ta da kafafun ta ciki da waje,sannan wata matar kuma ana yan yan kata da almakashin wuta wata kuwa tana da kan alade da jikin jaki kuma ana mata azabobi kala-kala, wata kuma tana da fuskar kare wuta na shiga jikin ta ta karkashin ta tana fita ta bakin ta kuma mala'iku na dukan ta da rodin karfe.
Sai sayyida Zahara(s.a) ta tambayi baban ta tace : yi mana addu'a ka fada min me wannan mata sukayi ake masu haka? Sai manzon Allah (s) yace: ki saurara ya abar kaunata! Ita wadda aka sarkafe ta da nonon ta tana hana mijin ta damar ya sadu da ita ne! Wadda aka sarkafe ta da kafafun ta kuwa tana fita daga gidan mijin ta ne ba tare da izinin sa ba! Ita kuwa wadda take cin naman jikin ta tana yin kwalliya ta gyara jikin ta don ta nunawa mazajen da ba nata ba! Wadda aka sarkafe hannuwan ta da kafafun ta tare da macizai da kunamu na cizon ta, bata damu da tsarkake kanta ba daga najasa kuma bata kula da yin wanka yayin daukewar hailar taba da bayan jima'i akan lokaci ba Wanda wannan yana nufin bata dau sallar ta da wani muhimmanci ba.
Ita kuwa bebiya makauniya tana haifar 'ya'ya ta hanyar zina amma sai tace na mijin ta ne, wadda ake yanka jikin ta da almakashin wuta kuwa bata kula da sanya hijabi agaban Wanda ba muharramin taba, wadda ake kona jikin ta kuma tana cin hanjin ta to tana kai wasu mata ne ga mazaje don biyan bukatun su. Ita kuwa wadda ke da fuskar kare kuma wuta na shiga ta karkashin ta tana fita ta bakin ta mace ce mai bakin kishi. Sai manzon Allah (s) yace: bakin ciki shine sakamakon macen da take batawa mijin ta rai farin ciki kuma na jiran wadda ta sanya shi farin ciki.
Duk kanin wadannan yanayi da manzon Allah (s) ya bayyana mana na wahalhalun da rai zai fuskanta a barzahu kafin tashin kiyama ne, bala'o'in lahira sunfi wannan zafi da wahala.
Abinda ya kamata ma'aurata mu kula dashi shine mu kasance masu kyautata zato ga juna mu zama masu yi ma juna uzuri, sannan mu kasance masu mutunta juna da mutunta iyayen juna, sannan mu kula da hakkokin juna Wanda suke na wajibi.mu kasance masu hakuri domin manzon Allah (s) yace: duk namijin da yayi hakuri kan cutarwar matar sa Allah zai bashi lada kamar na annabi ayuba (a.s) sannan duk matar da tayi hakuri kan cutarwar mijin ta to Allah zai bata lada kamar na asiya matar fir'auna.
To insha Allah mu hadu a rubutu na gaba mai taken DABARUN ZAMANTAKEWAR AURE.
AUTAR MARUBUT: sakina Ahmad
*MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE*
Tags:
Tunatarwa