DUNIYA BA A BAKI AMANA

✍️

ISHAQ SAGIR MAGAJI



Duk wanda ya ba wa wannan mata (duniya) amana to, haqiqa zai yi nadama.

 Domin ba ta da tabbas, ba ta ragawa ko ta sassautawa bawa yayin da ta yi shirin maka shi da
qasa.

 Ita dai mayaudariya ce, idan ka aure ta itace zata sake ka idan ma kai baka sake ta ba, nawa ta saka a idonka kana kallo d'an'uwa! To, kaima kayi taka-tsantsan da ita, shekarun da zata d'an ara maka 'yan kad'an ne, shekaru hamsin sittin ko saba'in ne, a cikin su idan kai mai wayo ne sai ka ribace wajen gina haqaiqanin gidanka na tabbas wato (gidan lahira).

 Yanzu zaka had'a shekaru hamsin, sittin ko saba'in da shekaru har abada?

 'Dan'uwa ka sani shekarun da zaka yi a duniyar nan na d'an jin dad'inta (idan ma kana daga cikin masu d'an jin dad'in) shekaru hamsin ne ko sittin ko kuma saba'in.

 Su ma shekarun ba a gaba d'ayansu ne zaka ji dad'in ba, a'a a wasu daga cikin su ne.
 Domin tun daga lokacin da aka haife ka har lokacin da balaga tazo maka ai baka san komai na gard'in duniya ba don ba ka ma da hankali.

 Tun daga lokacin da ka balaga har lokacin da ka kai d'an shekaru arba'in ai ba kan wani dad'in duniya ba, domin kana cikin gwagwarmayar tara abin duniya ne domin 'ya'yanka.

 Kafin ma ka kai haka! A baya kana cikin gwagwarmayar neman ilmi ne ko koyon sana'ar da zaka riqe ka rufawa kanka asiri.
 Ka kammala karatun ko koyon sana'ar, ka bazama neman aiki da kafuwa a sana'ar, duka fa wannan ba'a ma samu duniyar ba gwagwarmaya kawai akeyi.

 Duniyar ta samu (idan ma an dace) a lokacin da ake shirin miqe qafa a lasa sai mutuwa ta qwanqwasa qofa kuma dole a bud'e, idan ma mutuwa ba ta zo ba dole tsufa ya doka sallama (Ya Sallam).

 Yanzu don Allah d'an'uwa akan wad'annan 'yan shekarun na duniya masu cike da wahalhalu da tarnaqai iri-iri zaka yi sakaci da rayuwar da bata da iyaka? (Rayuwar lahira)?.

 Ai mai lafiyayyen hankali da qwaqw-Qwaran tunani ba zai yarda akan wannan gajeruwar rayuwar ya 'barar da rayuwar aljanna ba, zai dage iya wiya yaga yayi nasarar cancantar shiga wancan gida na lambu da kayan morewa rayuwa da gwangwajewa (gidan aljannah), ba zai bari ya watsarda gidan sa na din-din-din akan wannan gida wucin gadi ba.

 Allah ya bamu ikon yin anfani da wannan gida na duniya wajen samun rayuwar hutu da jin dad'i na gidan aljannah, ya bamu ikon yin watsi da sha'awowi na wannan gida wad'anda ke sabbabawa bawa afkawa haramun da kusa-kurai.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post