_cewar khalisat A. Dam
Daga shafin Ma'asumah news updates*
shakka babu soyayyar gaskiya ga masoya ita ce
soyayya, bugu-da-kari, soyayyar da ta ginu akan
turba ta gaskiya ita ce soyayya, ba haushe na cewa,
dana sani keyace tabbas haka abin ya ke.
Allah ya (T) ya yimin ni'ima wacce duk kan wata
mace zata yi burin ta sami, irin ni'imar da na samu,
na kasance, mace mai kyawun gaske wanda idan
ana maganar kyawawa ina daya daga ciki idan ba'a
sani ta biyu ba to xanzamo ta Uku to. Baya ga haka
Allah (T) ya a zirtani da miji, me mutukar kaunata,
duk yadda aka kai da maganar so, mijina ya
nunamin so, mutuka da gaske, domin son da ya ke
min ya fi nawa ne sa ba kusa, baya ga haka Allah
ya shi mai kudi, dai dai bakin gwargwado.
Mahaifina ba wani mai kudi ba ne, face dai ya na
da rufin asiri, duk da cewa wasu lokutan sai yaje
kasuwa, ya kasa kayan da yake sai dawa, sannan a
iya samin abin da xa'aci, lokuta masu yawa mijina
shike tallafawa iyaya ne dari bisa dari kama suturar
su, abincin su, dasauran su kafin abinci ya kare
yasa an kai mu su wasu Baya ga haka mahaifina ya
na da mata biyu, kuma Alhamdullah Allah ya bashi
yaya duk da haka, mahaifin mu baiyi wasa, da
tarbiyar mu ba, haka kuma bai yi wasa da karatun
mu ba, duk abin da yara suke bukata a rayiwa, sai
dai na ce Allah ya sa ka masa da alkhairi.Domin ya
yi kokari mutuka gaya akan mu, haka xalika maman,
mu duk da cewa ita ce uwar gida amman ta bamu
tarbiya iya ka iyawarta. Ko da yake ban fito a gidan
masu kudiba, amman na kasance mai san abin
duniya da sha'awaice-sha'awanta, domin kunsan
yayan talakawa mafi yawa duk inda muka sami wata
dama munfi daga kai da nuna mu wasu ne.
Shakka babu mijina ya kasance namiji me hakuri da
kawar da kai, amman sai dai kash! kusan soyayyar
da na ke masa mafi yawan domin abin kudin da ya
ke da shine, ko da ya ke mubarak nasan da cewa,
ni ba'ajin sabace domin Allah ya yimasa farin jinin
yan mata sosan gaske, masu kudi amman duk da
haka ya watsar da su ya dauki yar talaka wanda kai
kasan soyayya gamanjini ce, amman ni nasan shi
ba ajin sa bane. Ya rikeni tsakani da Allah ya kuma
nunamin soyayya tabbas ni ma ina san sa, amman
bai kai, san da ya ke min ba. Mijina ko nawa na
bukata ya kan bani, kuma komai na ce ya siyamin
ya na siyamin, wani abin alfaharin ma, duk da yadda
mata suke rubu-binsa amman shi ko ajikin sa, bashi
da bukatar kara aure, ko kusa. Ya kasance dan
kasuwa wanda Alhamdullah Allah ya yimasa nasibi
akan kasuwanci sa, wanda kaf dan ginsu shi yake
tallafa musu, dumin shi abin sa, bai rufemasa idon,
ya taimakawa muta ne da yawan gaske.
Tabbas, duk inda aka kai ga nuna soyayya ina
nunawa Mubarak soyayya, duk inda aka kai ka shiga
daula dai dai bakin gwargwado Allah ya dan damin.
Ko da ya ke Allah ya azirtamu da yara 3 wanda
suna samun kulawa daga bangaran sa da kuma ban
garena, kawayena kuwa kowacce sai san barkata ke,
da Allah yasa na yi da ce da miji na kwarai, mai
sona me kuma san dangina, duk da cewa Allah shi
ne shaida bantaba, xuwa wajan wani malam ko
bokaba akan mubarka ba, ko dan kar ya kara aure
ko wani abu me kama da haka, muna zaune lafiya
babu wata matsala abin mu gwanin bansha'awa.
A kwana a tashi katsaham sai Allah a jarabci mijan
matukar jarabta, har sai da takai abincin da zamuci
ya yananeman ya fi karfin mu, karatun yaran mu,
kuwa sun dawo gida da xama sabo da ba bu kudin
da xa'abiyamu su, wasu lokutan yayan sa, shike
tallafamasa, musabbabin kuwa fadawar sa
jarrabawa abu biyu ne, ba'ajima da yi masa, 419 ba
na kimanin wasu miliyoyi katsaham kuma aka
yimusu gobara a kasuwar da ya ke kasuwancin sa,
wanda bai jima da dawowa daga chine ba, anyi
sabon siyayya amman cikin kudirar Allah gobara ta
lashe katinsa gabadaya kaf. Ko da ya ke Mubarak
mutum ne duk inda ake maganar mutum me
takawa, da biyayya ga iyaye, da fitar da hakkin
Allah mubarak ya kai, badaban ina da karfin
imaniba sai, kwakwalwar sa ta tabu, amman ga ba
daya ya bi, ya fauwala Allah, haka duk kadarorin sa
suka kare, Abin abin ban tausayi, yan uwa kuwa tun
daga dangina da danginsa, sun tausaya masa
mutuka da gaske, kuma su kansu sun san, mubarak
ya shiga wani yanayi.
Bayan wasu shekaru abubuwa sunki gaba sunki
vaya, hatta abincin da muke ci ba'acewa komai, da
yake ya yaye yara da yawa lokuta masu yawa su
suke tallafamasa. Domin shi mutum ne me kana'a
ba xai je ya ce abashi ba, haka dai muke lallabawa
Duk da irin halin da mubarak ya shiga amman a
wasu lokutan na kance ya yimin wasu abubuwan,
gashi ana fama, da yau da gobe, duk da cewa a
gaskiyar magana yayin da mubarak yarasa duk abin
da ya mallaka ba wani abu da ya tsira face gidan
da mu ke ciki shi kadai ne ya tsira. Haka lokaci
guda naji ba na ra'ayin sa kuma ba na san sa, bani
da ra'ayin rayiwa da shi, shi kuma gashi ya na
mutukar sona kamar kamar me, wanda gaskiyar
magana soyayyar da na ke masa kashi 2 cikin uku
domin abin da ya ke da shi ne, shi kuma domin
Allah ya ke sona, haka lokaci guda na sauyamasa,
memakwan na kasance me kwantar masa da hankli
da lallashin sa, amman ni duk ba na tunanin haka,
wanda ni inda hali ya sauwakemin na je na auri
wani, domin ni baxan iya rayiwa a cikin kangin
talauciba, haka ya kasa gane gaba da bayana. Tun
danginsa musamman mahaifiyar sa basu gane ba,
haka suka fara fuskantar ba ma xaman lafiya da
Mubarak, duk da cewa uwar sa ta na mutukar sona,
ta buga ta raya ko da akwai wani abu da Mubarak
ya ke min? haka xan kirkiri wani abu na fada, wanda
bai kai abuba amman haka xan kara gishiri da
magi. Karshe idan an sulhunta kwana biyu, sai na
koma gidan jia domin ni kawai burina ya
sauwakemin, haka xaije ya jan iyayana domin su
yimin nasiha amman duk na sihar su a banxa.
Ranan katsaham mubarak ya fita ya dawo a gajiya
an dan sami abin da xa'a karya da safe, na dube
shi batare da sannun da xuwa, na kawo masa dan
abin da na dafa, duk da haka shi gaisheni na amsa
aciki, haka na shiga daki na fito na ce da shi, ko
kasan bikin balkis ya na karatowa, kuma maganar
ankwannan har yanxu shiru banji kana maganar
saba, sannan kasan bamu da man shafawa da
sabulu sannan kayan kwalliyata suma sun dakko
hanyar karewa, shima na gayama har yanxu na ji
bakace komai ba. daga fada mubarka ya duban
cikin bacin rai wanda na jima banga bacin ransa ba
irin wannan rananar ban ankaraba na ji ya ce dani
khalisat? wai kuwa kinsan me ki ke fada? cikin
bacin rai ya mike abincin da bai karasa ciba ya
barshi, ya nufi dakinsa, amman duk da haka na
tashi na bishi, a cikin fushi.
*Muhadu a kashi na biyu*(2)
Don jin ya xata kaya.
*Daga dan uwan ku Habib Rabiu Nasralla*
Emai:habibrabiu81@gmail.com