Babu hikima ga maza ko Hankali masu ra'ayin Zama da macce Daya.....
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
A RIQA YIN TUNANI CIKIN RAYUWA
Babu hikima kuma babu hankali ga maza masu ra'ayin zama da mace daya (1) ko kuma matar da ke tunanin ba za ta iya zama da 'yar'uwarta ba wacce aka fi sani da (KISHIYA).
Tunda Allah (T) yayi umarni ga masu iko cewa zasu iya auren mata 2,3-4, sannan Manzon Allah (S.A.W.W) ya aikata a aikace, ya kamata ga mai hikima da hankali yayi tunanin wani babban al'amari da ake fuskanta (qarancin maza da yawan mata).
Magana ce ta gaskiya, kowa yayi dubi zuwa ga yaran da ke cikin gidansu ya gani, shin 'ya'ya maza ne mafi yawa ko kuma 'ya'ya mata?
Na'am, wani gidan za a tarar 'ya'ya maza sunfi yawa, amma da za a qididdige adadin 'ya'yan da ke cikin gidaje 10, to, za a tarar bakwai bisa goma 7/10 mata ne, kashi uku sune maza daga cikin su.
Idan muka dawo kanmu a dai-dai-ku za ka iya ganin mace 1 na da 'ya'ya mata uku Riss a jere gabanta, banda na wani dakin, kuma qaramar cikinsu ma ta isa aure tun shekaru uku da suka wuce, amma babu wacce aka aurar daga cikin su, alhali ba karatu suke ba. Ko da ma suna karatun sai ka ji ana cewa rashin mijin aure ne.
Haba jama'a, Allah ya bamu hankali ne fa don muyi tunani, amma tunanin wasu kamar na dabbobi ne.
Idan kace kai da mace 1 za ka zauna, ko kice ba za ki zauna da kishiya ba, to, dan Allah a tunaninku kun yiwa 'ya'yanku adalci?
Domin idan kowa yace ya qyamaci zama da mata fiye da 1, to, 'ya'yansu mata ma za su zauna matuqar kowa zaiyi koyi da shi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
~26-9-2019 - 27-1-1441 (A.H)