✍️ALIYU DAHIRU ALIYU
Tun ranar da BBC Hausa ta saka rahoton malaman Shi’a da suke aurar da kananun yara ta hanyar mutu’a ake ta turo min sakonni kan na yi magana akai. Ni ta fuskar da na kalli abin ba ta haramci ko halacci ba ne. Na kalla ta fuskar cin zarafin kananun yara da ake yi da sunan addini ne. Wannan kuwa har Ahlussunnah sun yarda da auren har yar shekara 6 kuma a yi jima’i da ita a 9! Rigimarsu da Shi’a kawai a bangaren sabanin haramci da halacci ce ba wai a ainahin cutar “paedophilia” da take damunsu ba.
Idan maganar mutu’a ce to ina kallonta ta wata fuska ta daban. Masana halayyar dan adam sun nuna cewa kwakwalwa ba ta iya zama sai da abubuwa guda uku: abinci, bacci da jima’i. Wadannan abubuwan a jere suke guda uku da matukar ka wuce matakin abinci to za ka so yin bacci, daga nan kuma sai neman jima’i. Watakila dalilin da ya sa kenan binciken da aka buga a Daily Mirror da fassarar a BBC Hausa ya nuna manoma sun fi kowa yin jima’i, saboda da sun ci sun koshi sun huta to kuma jima’in ne zai zo ransu.
Babu ta yadda dan adam zai rabu da jima’i. Idan ya rasa wata hanyar to zai nemo wata. Ba wani ne yake koyawa matasa “masturbation” ba, don haka larabawa ma haka suke kiransa da “Adatus-sirriyya”. Ba abin mamaki ba ne da ake ta binciko makarantun allo na mari ake samun almajiran suna luwadi a tsakaninsu. Duk lokacin da babu wani jinsi to jinsi za su dinga neman junansu. Neman jinsi, tsakanin namji da namiji ko mace da mace, abu ne da yake ruwan dare a tsakanin wadanda basa gani ko samun wani jinsin sosai. Misali: gidan yari, sojoji a lokacin yaki (don haka suke fyade bayan sun ci gari), matan da aka hanasu ganin maza ko cudanya da su, mahaya jirgin ruwa da suke watanni basu dawo gida ba, da dai sauransu da bincike ya nuna.
Al’ummomi suna da hanyoyinsu da yawa na kin yin aure amma kuma da shigo da hanyoyin jima’i don saukakawa bukatunsu. A zamanin baya a Russia an yi abin da ake kira da “sexual communism” da maza da mata ke yin jima’i kyauta ko da babu aure. A garuruwa da yawa za ka ga akwai gidajen karuwai da gwamnati ta bari domin wadanda ba za su iya aure ba su tafi can su lalace. Masu halatta mutu’a suna ganin irin hikimar ce ta janyo Musulinci ya ce a yi aure zuwa wani lokaci sai a rabu domin a biyawa juna bukata kuma yayan da aka haifa su san suna da iyaye, ba kamar a karuwanci ko a “sexual communism” ba. Aure kam a tsakanin musulmi ya yi tsada sosai ta yadda wasu hanyoyin fitar da bukatar sun fi shi sauki a tsakaninsu.
Hatta Alhussunnah (musamman Salafiyya) sun yarda da wani aure da ake kira “misyar” ko “misfar” da babbar manufarsa ita ce jima’i, ba kamar sauran auren da ake yi ba. Wadanda suka halatta mutu’a suna yinsa a mafi yawan lokaci a lokacin da suke matasa kuma suke tsakiyar sha’awa, musamman a jami’o’i. Suna ganin a wannan yanayi mutu’ar ce kawai za ta kare matashi daga fadawa zina da karuwanci. Ana yin auren mutu’a a bainar jama’a da shaidu sosai ba wai buya ake ana yi kamar yadda wasu suke zato ba.
Meye matsalata da mutu’a? Ni ba haramci ko halacci ne matsalata da auren ba. Sabani ne da ko a cikin mazhabobin sunnah akan samu sabanin haramci da halacci. Sannan akwai halaccin da ba zan so na yi ba kamar sakin aure. Matsalata da auren mutu’a shi ne dorashi da aka yi kacokan akan jima’i kawai.
Da a tsakanin auren akwai soyayya da tausayi (muwaddatun warahma) kamar yadda Allah ya sanya aure, da ba ma za a yi tunanin saka masa lokaci ba. Idan da ana yin auren da niyyar soyayya da jin kai amma sai ya zama cewar rabuwar gari za ta iya raba auren bayan wani lokaci, kamar a ce tafiya ta kama mutum ya tafi wani gari (kamar yadda yake a “misfar”), to abin zai zo da sauki. Amma a saka jima’i a matsayin tushen auren mutu’a to shi ne zuciyata ba ta kwanta da shi ba.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
Meye matsalata da mutu’a? Ni ba haramci ko halacci ne matsalata da auren ba. Sabani ne da ko a cikin mazhabobin sunnah akan samu sabanin haramci da halacci. Sannan akwai halaccin da ba zan so na yi ba kamar sakin aure. Matsalata da auren mutu’a shi ne dorashi da aka yi kacokan akan jima’i kawai.
Da a tsakanin auren akwai soyayya da tausayi (muwaddatun warahma) kamar yadda Allah ya sanya aure, da ba ma za a yi tunanin saka masa lokaci ba. Idan da ana yin auren da niyyar soyayya da jin kai amma sai ya zama cewar rabuwar gari za ta iya raba auren bayan wani lokaci, kamar a ce tafiya ta kama mutum ya tafi wani gari (kamar yadda yake a “misfar”), to abin zai zo da sauki. Amma a saka jima’i a matsayin tushen auren mutu’a to shi ne zuciyata ba ta kwanta da shi ba.
Tags:
Daga marubata