Ashe Haka Dan Danon Dacin Yaudara yake!!?

cewar khadijat A kamal

_Daga shafin Ma'asumah Nigeria News updates

Ya na yi me ban takaici, tare da alhini maras
misaltuwa, ban san da cewar haka dacin yaudara ya
ke, ko da ya ke nakanji kawaye na wasu daga cikin
su na hirar amman bansan wanne irin dacin bakin
ciki zuciya take dan dana ba.

 Ko da ya ke gaskiyar
magana santsin soyayya ya debeni wanda bazan iya
misaltawa ba, ko da yake shakka babu na yi
kuskure babba a rayiwata.
Na kasan ce mace me kyawun gaske baya ga haka
Allah ya yi min farin jini dai dai bakin gwargwado.
Haka zalika Allah ya azirtani da samari dai dai
gwargwado, Ko da ya ke na so ace na bayyana ya
na yin mu'amalata da sauran samarini, amman sai
dai kash! ba na san na tsawaita sabo da lokaci.

A irin wannan ya na yi, akwana a tashi Allah ya hada
dani da wani saurayi me nutsuwa, kwarjini, iya
magana, kamin kai, hakuri uwa uba ga shi ya na da
ilimi dai dai bakin gwar-gwado, nasan da cewa me
karatu zai so jin sunan sa. ba komai ne sunan sa
ba face KAMAL. Mun fada soyayya da shi tun
bayan haduwa ta da shi a lokacin da na je bikin
wata kawata me suna saudat. Sakamakon ya na yi
lokaci ba zai yiwu na fayyace komai da ko mai ba
Sakamakon ya na yin lokaci.

Bayan haduwa ta das shiduk da ya ke na ja ajin sosai gaske haka kuman nayi masa wulakaci da ban da ban, wanda nasan
ba duka da na mijine zai iya jurewa ba, duk da
cewa kun san da cewar ba haduwar farko ne mace
ta ke jin soyayyar wani ta shiga zuciyar ki, dole sai
a hankali. Sakamakan irin abin da na ke yi masa
gaskiya ya yi yawa, hakan yasa na fara sauyawa,
duk da cewa ina san shi, amman ba sosai ba.
kunsan maita irin ta da namiji duk irin abin da
zakiyiwa namiji sai ya jure domin dai ya sami
soyayyar ki. Ko da ya ke farkon haduwar mu na yi
masa kwatancan gidan mu dakyar domin gaskiyar
magana kamal saurayine na mijin gaske. A haka
wasa wasa soyayyar mu ta fara yin nisa, ko da ya
ke hakika ina da masoya sosan gaske. Amman
soyayyar kamal ta fi tasiri fiye da sauran samarina,
sai dai kash! kamal shi mutum ne wanda bashi da
abin hannu, amman duk yadda zai yi kokirin
farantamin rai dai dai bakin gwargwado.
Kamal ya nunamin soyayya mutuka da gaske,
wanda na yi burin a ce ya kasance majina na har
abada. Amman gaskiya ni aburina ina san na auri
mutumin da ya ke da abin hannu, duk da yake a
cikin samarina akwai masu da shi, amman gaskiya
soyayyar su batai min ba. Maganar mu ta fara nisa
domin iyaye na da na kamal, duk sun san soyayyar
mu, wanda ana kokarin kawo kudina domin magana
ta yi nisa, Katsaham sai Allah ya hadi da wani,
matashi me suna Sadiq.

 Sadik matashi ne wanda a
gaskiyar magana iyayan sa masu kudine kuma Allah
ya hore masa iya kalami da jan hankali ga ya mace,
domin ya fi kamal nesa ba kusaba, kun da cewar
duk da namijin da ya fiya kal-kal da harshe to kiji
tsoran sa, amman ina wanda ya yi nisa baya jin kira,
duk ban yi lakari da hakan ba, haduwar mu da
sadik ta farko na hadu da shi, a lokacin da na raka
kawata Rukkaya gidan biki. Abu kamar wasa
bansan lokacin da soyayyar sadiq ta shiga zuciyata
ba, ana haka naga na sami wanda ra'ayina ya ke so,
ban dobi tarbiyyar sa ba, tsoran Allah sa, da duk
abin da ya kamata na duba ba, sam sam ban duba.
A kwana a tashi, soyayyar kamal ta fara rauni a
cikin zuciyata, haka na fara sauyamasa, wanda ko
da yaushe ina kokarin na sami laifin da zai yimin ko
ya ya wanda zan fake da shi, domin mu bata domin
na sami wanda ya fishi, batare da tuna irin soyayyar
da ya ke yimin ba sabo da Allah. Karshe na
sauyamasa gaba daya, wanda ko da ya kirani sai
naga damar dagawa, duk irin hakurin sa har sai da
takai ya fita daga harkata, haka ya je ya sami iyaye
na domin aji me ke faruwa, baya ga kawaye na duk
inda zai bi, ya ji ta bakai na ni kuma na nuna bani
da ra'ayin soyayyar sa, iyayena son yi ya kar kokarin
su akai amman na ki ji, hakika kamal ya na mutukar
sona fiye da yadda mutum ya ke zato, domin irin
abin na yi masa har sai da takai, ya kwanta a
asibiti. Karshe dole ya hakura dani batare da zuciyar
sa ta na so ba. Abokan sa kam sun taka rawa
wajan ganin sun ji daga gare ni amman sam sam
duk abin da nasan zai hadani da kamal bana son
shi, duk da cewa wlh babu abin da ya yimin kawai
sakamakon na sami wanda ya fishi.

A kwana a tashi kamal ya hakura dani, ni kuwa da
ni da sadiq ba'acewa komai domin tuni soyayyar
mu, ta yi nisa kuma, domin kararaa sadiq ya
nunamina aurata zai yi, kuma ko mai na ke so
sadiq zai kashemin. Har sai da takai na bawa sadiq
kai na, wanda ku kasan matarsa domin ko me ya
nema a gareni ina yimasa, har sai da takai a gidan
mu an san shi. Haka muka dauki tsawan lokaci mu
na sheke ayar mu, wani lokacin zan nuna, zamuje
wani guri da zummar biki, sadiq zai je ya kama
mana hotel, mu je mu, sheke ayar mu. Domin duk
kan yarda na bashi. Ana haka mun dauki tsawan
shekara uku da watanni, da zimmar sadiq da ya
kammala Karatu za asha biki, kamar yadda ya
nunamin. A haka muka cigaba da soyayyar mu,
katsaham ban yi aune domin soyayyarsa sadiq ta
shiga zuciyata sosai na narke a soyayyar sa. Lokaci
guda ba tare da aune ba, sai sadiq ya fara
sauyamin, abu kamar wasa, zan kirashi amman sai
ya gama damar dagawa, a haka wani lokacin har
binsa gidaN su na ke, amman abu kamar wasa, ya
shiga wulakantani, batare da na yi masa laifin
komai ba, a kwai lokacin da na sami nasarar da ya
daga wayata, na fashe masa da kuka na ce sadiq
idan Baka da ra'ayina ka gayamin dan Allah sadiq,
kafin na karasa na dada fashewa da kuka, sannan
na ce kaji sadiq? ya ce ni, babu komai, yanzu ina
jin bacci sai da safe, ya kashe wayar sa, a ranar na
yi kUka kamar raina zai fita, amman duk da haka,
ban hakuraba, a daran na sake kiran shi, da kiran
wayar sa ke da wuya sai na ji, wayar sa akashe.
Na dai takai ta mu ku zan ce, ashe sadiq ya samu
wacce ta fine, haka ga ba daya ya fita daga
Harkata. Sai da takai ga na kwanta a asibiti, kamar
bazan yi, raiba.
Shi kuwa kamal sakamakon irin yaudarar shi da na
Yi, masa gaba daya soyyay ta fita daga ransa domin
ko budurwa bashi da ita.

Karshe haka na shiga kogwan tunani ako da yaushe.
HAkikA na yi bakin ciki sosai domin akan sadiq har
sai da takai ga na kori samarina domin ina ganin,
sadiq shi ne mijina. Gaskiya hausawa sun yi
gaskiya da suke cewa kwadayi mabudin wahala,
bansan da cewa hakA dan danan dacin yaudara y
Ke ba, kuma yanzu na fahimci cewar kamal shi ne
masoyina na gaskiya, domin duk runtsi duk wuya ya
na tare dani. Na sha yi masa alkawari ban san
adadibA na ce da ce kamal wlh kai ne wandA na
mallakawa zuciyata har abada kuma duk rintsi duk
wuya bazan sauya ba kamal.
A duk lokacin da na tuna irin wannan kalmomi da
na yiwa Kamal raina ya kan dugunzuma, yanzu gashi
samari na duk sun gudu, gashi kuma ina bukatar na
yi auran, shi kuwa sadiq tuni na sami labari daga
baya ma ya yi auran sa, shi kuwa kamal yanzu Baya
ma kasar Allah ya daga shi, ya na harkokin
kasiwanci, amman dai har yanzu bai yi aureba.

Sabo da haka ya ke yar uwata karda kwadayin
duniya ya rude ki, ki ko karin samun wandA ya ke
son ki, sabo da Allah. Ke ma ki soshi sabo da
Allah, hakika na yi dana sani a rayiwata. Akarshe ina
rokan Allah ya yafemin irin abin da na aikata abaya,
sannan kirana ga yan uwana mata ki guji duk na
mijin da zai bukaci wani abu da yasabawa shari'a
daga gare ku, ke ko da ko ya kawo kudi gidan ku,
domin ba aure akai ba.

*Me rubutawa Habib Rabiu Nasrallah*
Email:Habibrabiu81@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post