TSORON KAFUWAR DAULAR MUSLIMCI SUKE YI
Da shike muslimci addini ne na adalci sai ya tattaro mana dukkan tarihin magabata da irin abubuwan da ya faru dasu na cutarwa ko samun goyon baya.
Cikin tarihin an kawo mana irin cutarwar da aka yiwa Annabawa (A S) tare da qaryata su kan cewa su batattu ne, ba wai bisa suna zagin uban wani ko yin addinin da ba daidai ba.
Daga cikin su akwai:-
(1)- NUHU (A.S):- A lokacin da ya gargadi mutanensa don su tsarkake Allah sai masu fada a ji daga cikin su suka ce;
" LALLE NE MU HAQIQA MUNA GANIN KA A CIKIN BATA BAYYANANNIYA."
(A'ARAF:60)
(2)- SALIHU (A.S):- Shi ma abinda kangararrun mutanensa suka ce shine;
" LALLE NE MU, GA ABINDA KUKA YI IMANI DA SHI KAFIRAI NE."
(A'ARAF:76)
(3)- IBRAHIM (A.S) :- Game da shi mutanensa suka ce;
" KU QONE SHI, KU TAIMAKI GUMAKAN KU IDAN KUN KASANCE MASU AIKATAWA."
(ANBIYA:68)
(4)- YUSUF (A.S) :- Akan neman yardar Allah aka cutar da shi;
" ......Tace " MENENE SAKAMAKON WANDA YAYI NUFIN MUMMUNAN ABU GA IYALANKA? FACE A 'DAURE SHI, KO KUMA AYI MASA WATA AZABA MAI RADADI."
(YUSUF:25)
(5)- MUSA (A.S) :- Shi kuma,
" Fir'auna yace, " LALLE NE, NI INA YANYANKE HANNAYEN KU DA QAFAFUN KU A SABANI (qafar hagu da hannun dama), SANNAN KUMA HAQIQA INA TSIRE KU GABA 'DAYA."
(A'ARAF:124)
.
(6)- ISAH (A.S):- Game da mutanen sa Allah (T) cewa yayi;
" KUMA (su kafirai) SUKA YI MAKIRCI (don su kashe shi) ALLAH KUMA YAYI MUSU (sakamakon ) MAKIRCI, KUMA ALLAH SHINE MAFI ALKHAIRI (wajen yin hukunci akan) MAKIRAI."
(AL-IMRAN:54)
(7)- MUHAMMAD (S.A.W.W):- Shine wanda ya fi kowa iya wa'azi da kuma tausayi tare da yin kalmomi masu laushi don a gaskata shi, amma a hakan sai da aka yi nufin kashe shi bayan cutarwar da aka yi masa.
" KUMA (ka tuna) A LOKACIN DA WADANDA SUKA KAFIRTA SUKE YIN MAKIRCI GAME DA KAI, DOMIN SU TABBATAR DA KAI (a kurkuku), KO KUMA SU KASHE KA, KO KUMA SU FITAR....
Zamuci gaba
Daga Wakilinmu Ado Isah guda