AMAFANIN RAKE AJIKIN ƊAN ADAM

AMFANIN RAKE A JIKIN ƊAN ADAM.

Ma'asumah Nigeria News Update


A wannan yanayin ne zaka ga ana tallan
Rake a duk fadin garuruwan Arewa, Mutane kan kira masu rake su saya don zaki.
Amma amfanin Rake ya wuce nan, Ga wasu daga cikin amfanin Rake nan:

1⃣ Yana ƙarfafa garkuwan Jiki Yana
taimakawa wajen kare cutar sanyi, mura da
cutar daji.

2- Yana ƙara ruwan Jiki da ƙarfi musamman
ga masu aikin ƙarfi ko aiki cikin rana.

3- Yana taimaka ma Hanta, Zuciya, Ciki, Ido,
Kwakwalwa da Al'aura.

4⃣ Yana taimakon ƙoda wajen haɗa fitsari
da kyau.

5⃣ Yana gyara Fata saboda sinadarin glycolic acid dake cikinsa.

6⃣ Yana wanke Haƙora (amma yana da kyau
ka kuskure baki bayan kasha saboda
kwayoyin cuta na iya samun zakin a
matsayin abinci).

7⃣. Gara kasha Rake da ka sayi lemun
kwalba don yafi su amfani.

8⃣. Yana maganin yunwa kuma baya da illa
ga masu cutar ciwon suga.

Ma'asumah Nigeria News Update
 Ishaq Muh'd Suleiman

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post