*YADDA NA FAHIMCI HARKA ISLAMIYYA KARKASHIN JAGORANCIN SAYYID ZAKZAKY (H)*

Tare da Sakina Ahmad

MLM Ibrahim daurawa Daga hagu tare da C.E.O na shafin Ma'asumah mas'udu Dan Masani Shinkafi a wajen Taron karawa juna sani Karo na biyu a  garin kano


Hafsat sulaiman Ahmad shine cikakken suna na, amma ana kirana da ummee saboda sunan mahaifiyar banana ne naci, an haifeni a garin kazaure a unguwar Latin waliyay,nayi karatu na na addini dana zamani a garin kazaure. 
Wata rana na dawo daga islamiyya da yamma na gamu da wata kawata da mukai secondary school tare mai suna Fatima Yusuf. Fatima yarinya CE nutsattsiya ga hankali tunani da hangen nesa. Iran Fatima na magana cikin nutsuwa da hikima sai kayi tunanin wani babban mutum ne saboda akwai hikima acikin dukkan zancen ta. Allah ya hore mata baiwa da ilhama a bangarori da dama.

Bayan mun gaisa da Fatima sai take tambaya ta ya karatu? Nace Alhamdu lillah, nayi mata murnar saukar alkur'ani mai girma da tayi, ta nunamin farin cikin ta sosan gaske, tace min ummee zan wuce gida magaruba nayi kuma kinga a hanya muke! Nace mata gakane to sai anjima ki gaishe da umma, mukayi sallam, ta tafi nima na tafi da dimbin tambayoyi a raina! Don harga Allah dabi'un Fatima suna birgeni kuma duk wani abun batanci da ake danganta Fatima dama masu irin akidar ta in banga ko daya ba, har naje gida INA sakawa da kwancewa.

Daga baya sai na yanke shawarar tambayar Fatima duk abinda ake fada akan su (yan Shi'a) domin inji gaskiyar magana dama dalilinsu nayi. Wata ranar daba makarantar islamiyya na shirts kaima Fatima ziyara gidansu, agidan mu idan nace Fatima zan kaima ziyara to gaskiya ba za'abarni ba shiyasa nace zanje gidan su wata kawata maryam wadda gidansu a bayan layin su Fatima take.
Zuwa na gidansu Fatima shine ummul aba'isin sauyani dama duk wani gurbataccen tunanin da yayi tasiri a kwakwalwata domin kuwa ina zuwa na tarar da ita tana sauri tana shiryawa ga dukkan alamu kuwa wurin da zataje yana da muhimmanci sosai domin kuwa hankalin ta ya tashi kuma tanayi tana duba agogo. Wani Abu daya karamin kaunar Fatima shine duk saurin da take bai hana ta yimin tarba ta mutumci ba kuma naji dadin haka, shiyasa nace mata Fatima naga alama sauri kike kuma gaskiya tamboyoyi ne ke tafe dani amma insha Allah zan dawo daga baya, tace min to na gode sosai, nima zanje wurin zaman youth forum ne kuma gashi ta kusa makara, kawai sai naji INA da sha'awan bin ta.kawai sai naji tsinci kaina da fadin Fatima idan ba damuwa zan rakaki,ki aramin irin kayan ki nasa don kar a hanani shiga! Sai kawai tayi murmushi tace ummee ba mai hanaki shiga domin muna maraba da kowa mun dauki ko wane irin mutum abokin rayuwarmu musulmi da kirista kuwa duk namu ne. Sai nace mata to shikenan muje.... Daga gidansu Fatima zuwa wurin da suke cema markaz ba nisa don anan ne ake yin zaman.
Alokacin da mukaje mun tarar an fara zaman muka samu wuri muka zauna, sukaci gaba da tattaunawar su nidai yar kallo ce don bana fahimtar komai, daga karshe suka samu matsaya daya inda daya bayan daya suka ruka daukar alkawari wani yana rubutawa wannan abin ya burgeni sosai har nake cema zuciya ta to amma akace daga Iran ake kawo musu kudi suna yin komai amma kuma yanzu gashi naga da Kansu suke hadawa wallahi abin ya birgeni sosai. Akwai wani mutum Wanda baya daga cikin masuyin zaman domin shi ya manyan ta sosai, sai ya kira daya gada cikin masu zaman ya rada masa magana! Sai da kowa yayi alkawari sai wannan matashi yace: alhamdulillah malam masa'ud yace abinda yan uwa suka Samar shi zai cika abinda yayi saura. Wannan abun ba karamin tasiri yayi a zuciya ta ba, sai bayan mun taho hanya na gaza daurewa nace ma Fatima wai Fatima me zakuyi da wadannan kudin masu yawa haka? Sai tayi murmushi har hakoranta suka fito ta dafa ni tace: ummee zamuyi walimar 'yan gayu ne da sallah. Idan nace walimar 'yan gayu ina nufin da sallah zamu shirya taro saboda matasa masu zaman banza Wanda rashin gata yasa basu tsaya sunyi karatu ba har suka fada hanyar shaye-shaye, to a irin wannan walimar da zamu hada musu akwai lecture sosai da za'ayi masu Wanda zata nuns musu illar wannan shaye-shaye da suke cikin hikima ba tare da sunga an kira su bane don aci mutumcin su ba, kuma duka muke hadawa mazan su da matansu, zakuma mu nuna musu mu malamin mu bai koya mana kyamatar suba kamar yadda al'ummah  take gudun su ba, saboda irin haka sai kiga wasu sun daina wasu kuma sun rage to kinga ai anci gaba, yau da gobe sai kiga an rage adadin yawan masu shaye-shaye. Wannan shine kawai ki naga ana hada kudi.

Wannan karon banyi kasa a gwiwa ba na tambaye ta, to amma kuma akace daga Iran ake turo maku kudi? Sai tace wannan ba gaskiya bane mai fadin haka yana fadar ra'ayin kansa ne amma babu masu kudi da ake turo mana daga kowace kasa, duk abinda kikaga munyi ginin makaranta ne, shirya maulud ne da duk wani Abu Wanda za'a kashe kudi to muna Samar da kudin ne a tsakanin my amma ba gaskiya bane cewar ana kawo mana kudi daga wata kasa. Nace mata na gode kuma na fahimta insha Allah zan dawo da sauran tambayoyi na don wannan na gamsu da amsarki kuma na yarda tunda na gani da ido na. Nayi mata godiya sosai mukayi sallama na tafi gida.
Bayan wasu kwanaki Fatima ta kawo min ziyarar bazata, nayi matukar mamakin irin shigar da ta zomin da ita, duk da daga baya ta fadamin hikimar ta nayin hakan. Ba wata Shiva bace tazo minda ita face irin shigar makarantar islamiyyar mu, wato dogon hijabi har kasa mai hannu da safa sai nikaf, a kofar gida suka gaisa da mahaifi na mai ra'ayin rikau akan akidar sa ta sunnah, ya sanya ma Fatima albarka tafi cikin kwando tare da jaddada min irin kawayen da yake so nayi mu'amala dasu kenan. Umma ta ma tayi farin ciki da kasancewar Fatima kawata duk da cewar basu Santa ba amma sunsan ahlin gidansu don yan gidansu ba boyayyu bane. Nayi mata jagora har zuwa dakin mu na kawo mata ruwa tasha muka fara fira, acikin firar ne nake ce mata: Fatima ba don kinyi irin shigar nan ba yau da nashiga uku a gidan nan! Fatima tace nima nayi tunanin haka shiyasa nazo a haka. Yauwa wai dama wace irin tambaya ce kike son yi min? Sai nace mata wallahi Fatima dama abubuwan da ake fada mana ne a makaranta suke daure min kai, kuma ni sai nake ganin kamar ba haka bane! Sai tace min me kenan? Sai nace mata: cewar kuna zagin sahabbai, kuma bakwa son ummul mu'uminuna Aisha (ra) sannan kuma a toilets dinku na babbar makarantar ku dake Zaria akwai sunayen Abubakar, umar, da usman sai kun taka su sannan kuke shiga toilet din? Sannan kuma Ku kafirai ne bakwa sallah a idon mutane ne kawai kuke nuns kunayi, kuma Ku yan fitina ne wannan kuma kuna bada aron Mayan Ku ayi auran matu'a dasu.
  Naga Bacon rai sosai a idon Fatima amma ta danne! Tayi ajiyar zuciya tace min ummee bakya bina bashin rantsuwa to wallahi, tallahi, billahillazi laa'ila ha illahuwa duk abin nan da kika fada karya ne ba daya daga ciki da akeyi. Tace zanmiki bayani daya bayan daya yadda zaki fahimta bani aron kunnen ki da nutsuwarki kuma duk abinda baki fahimta ba ki tammaye ni, tace mudau maganar zagin sahabbai:- ina kyautata a garin nan kika girma kuma muna gabatar da program a unguwar nan taku da rana daya kin taba jin an zagi wani sahabi? Nace mata a'a ta hanyar girgiza mata kaina, tace dakyau yan Shi'a basa zagin ko wane sahabi kuma basu taba zagin su ba kuma har abada bazasu zage su ba. 
 Abinda yan uwan mu ahlussunnah suka gaza ganewa shine fifita iyalan gidan manzon Allah (s) sama da kowa basa hada darajar su da ta kowa kuma duk abinda suke fada sun gani ne a litattafan ahlus sunnah, tambaya idan ba'a so a fada me yasa aka rubuta? Kai in takai ce maku daya bayan daya saida Fatima tayi min bayani sosai na fahimta. Daga karshe ne na tambayi Fatima alfarmar ta rika fadamin duk wani program da za'ayi insha Allah zanje, ta kuma cika alkawari domin kuwa duk wani taro da za'ayi sai ta fada min kuma sai naje. Sai dai ba a sani ba agidan mu. Ta sanadiyyar kawata Fatima na fahimci harkar nan har nayi nisan da bana jin kira nayi ma Allah alkawarin zan ci gaba dayi har zuwa ranar da yan gidan mu zasu fahimci wacece ni kuma koda zasu rika yagar naman jikina saboda azabtar wa to bazan fasa ba har zuwa lokacin da zasu fahimci gaskiya suma.

*YAN GIDANMU SUN GANONI*

Rana mai dimbin tarihi a rayuwa ta ranar da bazan manta da ita ba itace ranar 10 ga muharram narar ashura kenan, itace ranar da yazid bn Muawiya (l.a) ya tura rudunonin yaki Domin yakar imam Hussain, suka kuma yakar har suka kashe shi da duk wani masoyinsa ciki harda jinjirin da baisan komai ba, a irin wannan ranar duk duniya ta dau zafi musamman ga masoya iyalan gidan manzon Allah (s). A garin mu ma haka anyi majaalin azaa, da safe da yamma kuma muka fito don fada ma duniya ai nahin abinda ya faru sabanin abinda ake fada masu! A cikin muzahar sai naga yaya na da saurayina suna kallo yayana bai ganni ba amma shi saurayi na ya ganni don shine ma ya nunawa yayana ni! Nasan sun ganni kuma sun San na gansu hakan ne yasa bayan an tashi ban cire bakin hijabi na ba na nufi gidanmu.
Da zuwa gidan mu na tarar da mahifina da mahaifiyata a tsakar gida, nayi sallama ba Wanda ya amsamin, na yunkura zan tashi sai ga yaya na,ban Ankara ba naji saukar mari ta ko'ina karshe yaji Marin bazai masa ba ya hau dukana kai kace wani sa'an sa yake duka! Tun ina iya kuka har takai ga ko idona bana iya dagawa, Allah sarki soyayyar ya da mahaifiya, itace tasa mahifiya ta kokarin taimako na amma mahaifina ya hana ta, dishi-dishi na rika kallonta tana sharar hawaye ta nufi dakinta. Data nan ban sake sanin kaina ba sai bude ido na nayi na ganni tsakar gidan mu a yashe rana na duka! Na kar na samu na kai kaina dakin mu na kwanta ina kuka, kuma ko kadan banyi danasani ba, ban jima ba sai ga mahifiya ta tashigo dakin batace min komai ba ta wuce toilet din dake dakin mu ta hada min ruwan zafi ta fito bata ko kalli inda nake ba tace tashi kije kiyi wanka sai kawai ta fita, na tashi ina dafa bango har naje nayi wankan na fito naji kwarin jiki na.
 Tun daga wannan ranar na fara fuskan tar barazana a rayuwa ta kowa a gidan mu ya dai na kulani aka hanani fita aka kwace waya ta na shiga tasku kala-kala ciki harda fasuwar aure na amma duk da haka banji zan daina ba. 
 Allah sarki Fatima kawa ta gari itace take bani shawara akan in kara hakuri in ci gaba da yima iyaye na biyayya har zuwa lokacin da zasu fahimce in. Lokaci zuwa lokaci take aikomin da wasika ta hanyar wata yarinya yar unguwar mu. Kuma Alhamdulillah naga ribar yima iyaye biyayya domin kuwa a halin yanzu ni da dukkan yan gidan mu muna harka islamiyya kuma gashi har nayi aure harda Dana Muhammad jawad.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post