WANNAN ZALUNCINE !!!!

✍️
ALIYU DAHIRU ALIYU


Kenan bayan an kama shugabannin IMN na jihohi sai a dawo a bi mambobinsu kuma a kakkama? Wannan zalinci ne karara. Hukumomin da suka kasa komai akan masu garkuwa da mutane kuma suke sulhu da yan fashi da makami su ne suke kokarin kama wadanda babu abin da suka yi sai don kawai sun ce su yan Shi’a ne. Dama wannan na taba fada. Daga lokacin da aka ga kofa ta bude to shi kenan sai a fara zalinci daga kan wannan zuwa wancan. Wa ya san inda za a tsaya bayan IMN?

Wannan wani irin zalinci ne karara a idon duniya kowa yana gani ya yi shiru! Zalinci ga mutum daya dai-dai yake ga zalinci ga kowane mutum. Ragowar Musulmi kuma da suke jin dadin wannan rashin mutuncin da ake yi su ne suke ta maganar an rushe masallaci a Fatakawal ko an hana yan Kashmir da Rohingya yanci. Kowa azzalumi ne kawai sai wanda bai samu dama ba. Masu cewa basu yarda da abin da ake yiwa Palestine ba su ne kuma suke ganin dacewar abin da ake a Nijeriya. Allah ya wadaran munafukai. Allah ka sheda ba wannan addinin na munafukai nake ba.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 

Wannan magana ta ALIYU DAHIRU ALIYU ta biyu bayan Maganar Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu, inda yabada wani sabon umarni ga jami’an kasar da su rika bi sako-sako da lungu-lungu domin cafke manyan kungiyar IMN. IGP Mohammed Adamu ya nemi ‘yan sandan kasar su kamo masa Jagororin kungiyar nan ta IMN da aka haramta a Najeriya a dauk inda su ke. Shugaban ‘yan sandan ya yi wannan kira ne shekaran jiya.
 A wata takarda da aka sa wa hannu a Ranar Juma’a 30 ga Watan Agusta, IGP ya bada umarni daga Hedikwata zuwa ga Dakarun jihohi da shiyyoyin ‘yan sanda da cewa su kama duk manyan tafiyar IMN.
 ” Yanzu IGP Adamu ya sha alwashin ganin an takawa IMN burki a kasar.  Shugaban na Yan shia'a a Najeriya, Ibrahim Yakub El-Zakzaky ya na tsare a hannun hukuma tun karshen 2015. A yanzu kuma jami’an tsaro za su fara kama sauran Jagororinsa.  

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post